Neman gudunmuwar matasa akan zabe mai zuwa abu ne mai sauki idan har gwamnati ta shirya gina musu sabuwar Najeriya wacce zata inganta rayuwar kowa da kowa. Bincike ya nuna cewa matasan Najeriya sun kai adadin 38.1% a cikin adadin mutanen kasar (NPC 2010).
Babu shakka akwai kalubale idan akace wannan babbar kadara ba a moreta ba, ya zama wajibi matasa su shiga hayyacinsu, su gane cewa tarihi ya nuna mana cewa mafi rinjayen ‘yan mazan jiya da ake bamu labarinsu irin su Sardauna, Tafawa Balewa, Murtala Muhammad da sauransu sun samu dama ne tun suna kasa da shekara talatin da biyar (35 years). A wata majiyar ma an ce akwai shugaban kasar da Najeriya tayi sai bayan ya hau mulki yayi auren fari.
Gaskiyar lamari, zamu yi iya abunda zamu iya don ganin matasa sun zama masu amfani a kasar Najeriya saboda ko bayan babu rayuwarmu ‘yan baya zasu ji ko su karanta tarihin kokarin da mu kayi wajen shiryawa rayuwarsu kafin su zo.
Bamu ce sai kowa ya zama irin su Sardauna ba, to amma kai ma ba zaka so a barka a baya ba. Sai dai wadanda zamu yi koyi dasu din mun ji labarin cewa duk irin gwagwarmayar da suka yi sun samu Kwarin gwiwa ne daga kasar su. Abun da ya kamata shine, akwai bukatar mu duba irin gudunmuwar Najeriya ga wadancan ‘yan mazan jiya da kuma irin gudunmuwarta a yanzu ga matasan ta. Wannan ‘comparative analysis’ zai taimaka wajen yin abun da ya dace ga matasan yau.
Gaskiya na gamsu, mafi rinjayen matasan Najeriya suna son gyara, kawai dai masu qarancin ilimi daga cikinsu ne suke buqatar a bisu a hankali amma nayi imanin cewa idan har za a dinga shiga cikin lamarinsu; tabbas za a samu cikakken ‘demographic dividend’.
Wani abun ma da ake gani daga wajensu yana da alaqa da rashin kulawa a baya. Misali, lokacin da gwaunati ta fara bayar da dubu goma mafi yawancin matasan sai da suka koma suna yiwa gwaunatin Najeriya addu’a. Don ni na zauna da wasu daga cikinsu, saboda haka babu wata wahala a cikin dawo da hayyacin matasan Najeriya idan har gwaunati zata cigaba da tunani akansu.
Kuma Insha Allah zan iya fadakar da matasa dubu daruruwa a arewacin Najeriya. Don haka, duk matashin da ya shirya; ya ajje barandami ko gora mu hadu a akwatin za6e mai zuwa saboda babban makami a filin za6e shine babban ‘dan yatsanku.
Allah ya nuna mana zaben 2019 cikin zaman lafiya, imani, nasibi da rufin assiri.