A ranara Litinin Gwamna Abdul’aziz Yari na Jihar Zamfara ya yi ikirarin cewa an kammala zaben fidda-gwani na dan takarar gwamna da na sanatoci a jihar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa bayanin na Yari ya fito ne yayin da wakilan da uwar jam’iyya ta kasa ta tura domin ta gudanar da zabukan fidda-gwani a jihar Zamfara, ta ce ba a gudanar da zaben ba kwata-kwata.
Yari ya ce an kara gudanar da zaben ne tun da farko saboda kwanitin Abubakar Fari ya kasa gudanar da sahihin zaben fidda-gwani.
“Tunda dai tilas sai mun gudanar da zabe mun fitar da sakamako kafin 12 na daren 7 Ga Disamba, to mun yi abin da ake bukatar mu yi, kuma mun muika sakamakon zabe ga uwar jam’iyyar APC ta kasa.
“Amma ba mu san dalilin da ya sa kwamiti na biyu da aka sake turowa a karkashin Manjo Janar Mai Ritaya, Abubakar Mustapha suka yi abin da suka yi ba. Saboda ni dai na rigaya na bada umarnin a ci gaba da zaben fidda gwani tun a ranakun 1 da 2 Ga Oktoba.
Ya ce ya yi haka ne saboda shi ne jagoran APC na jihar Zamfara, don kada lokaci ya kure APC ba ta da dan takarar gwamna a Zamfara.
Gwamna Yari ya ce ya umarci shugaban jam’iyyar APC na jiha, Lawali Liman ya bayyana sakamakon zabe kamar haka:
Muktari Idris ne ya ci zaben dan takarar gwamna, Yari ya ci na sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma, Tijjani Kaura ta Yamma, shi kuma Aliyu Bilbis ta Tsakiya.
Sai dai kuma shugaban kwamitin shirya zabe da uwar jam’iyyar APC ta kasa ta tura domin ya gudanar da zabe, ya bayyana cewa, “mu dai a matsayin mu na wadanda APC ta tura domin su gudanar da zabe, ba a gudanar da wani zaben fidda-gwani a jihar Zamfara ba.
“Mu aka tura mu yi zabe, to ga dai kayan zabe nan a hannun mu, kuma za mu je mu damka rahoton mu ga sakateriyar jam’iyya ta kasa, wadda ita ce ta ba mu alhali da amanar zuwa mu yi zaben.
NAN ya ruwaito cewa a baya sau biyu ana tura kwamiti domin ya je ya gudanar da zaben fidda-gwani a jihar Zamfara, amma abin ya na cin tura.