Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta karfafa kawancen dake tsakaninta da hukumar hana yaduwar cututtuka na Afrika (CDC Africa) domin samar da ingantaciyyar kiwon lafiya wa mutanen nahiyar.
Jami’in WHO Matshidiso Moeti ya sanar da haka sannan ya kara da cewa sun amince da haka ne domin kubutar da mutane Nahiyar Afrika daga kamuwa da cututtuka.
” Sanin kowa ne cewa mutanen nahiyar Afrika na rasa rayukan su a dalilin bullowar cututtuka saboda rashin ma’aida hankali kan dakile bullowa,yaduwa da kawar da cututtukan.
” Inganta aiyukkan CDC Africa hanya ce da zai taimaka wajen samar wa mutanen Afrika da kariya daga kamuwa da cututtuka.
A karshe Kwamishinan tarayyar Afrika, Amira Elfadil da Jami’in CDC ta Afrika John Nkengasong sun yabi wannan shiri sannan sun ce za su ci gaba da taimaka wa kasashen nahiyar Afrika wajen tsaro hanyoyin da za a bi wajen dakile yaduwar cututtuka.