Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa gwamnati za ta gaggauta samar da zaman lafiya a hukumar inshorar lafiya ta kasa.
Adewole ya bayyana haka ne ranar Litini bayan dakataccen shugaban hukumar Usman Yusuf ya shigo harabar hukumar da karfi da tsiya.
Ya ce duk da cewa bai da cikakken bayyanai bisa abin da ya faru gwamnati za ta tabbata komai ya daidaita cikin gaggawa.
” Za mu zauna domin mu duba abin da ya faru yau a harabar hukumar inshorar kiwon lafiya sannan bayan haka zan aika wa sakataren gwamnatin tarayya duk abin da muka tattauna a kai.” Inji Minista.
Idan ba a manta ba a safiyan yau Litini ne ma’aikatan hukumar inshorar lafiya ta kasa NHIS suka yi cirko-cirko a wajen ofishin inda suka garkame kofar shiga don hana dakataccen shugaban hukumar, Yusuf Usman shiga harabar ma’aikatar ballantana ya kai ga ofishin sa.
Sannan a ranar Alhamis ne shugaban kwamitin gudanarwa na hukumar Enyantu Ifenne ta sanar da dakatar da Yusuf daga aiki sai Illa-masha’Allahu.
Kwamitin ta dauki wannan mataki ne bisa ga laifuka tara da Yusuf ya aikata a hukumar.
Enyanatu ta ce wannan matsaya da suka dauka zai samar wa kwamitin da suka kafa damar gudanar da bincike kan laifukan da Yusuf ya aikata.
‘‘Mu ba Yusuf damar tattara inasa inasa daga ofishinsa ranar Juma’a domin kwamitin ta sami damar gudanar da aiyukkan ta yadda ya kamata.
Sai dai kuma tun da sanyin asuba, Yusuf karyata wannan zargi da ake yi masa sannan a yau Litini ya tunkari ofishin sa da ‘Yan sanda kusan 50 inda da karfin tsiya suka shigar da shi ofishin sa.
” Sun yi mana feshin barkonon tsohuwa sannan sun yi kokarin harbin mu domin mun hana shi shiga ofis’’. Inji shugaban kungiyar ma’aikata, Omameji Abdulrazak.
Bayan haka wasu ma’aikatan hukumar sun yi korafin cewa shugaban shugaban kasa Muhammad Buhari ya sauke Yusuf daga aiki sannan ya kawo wanda ya fi dacewa a hukumar.
Bayanai sun nuna cewa a dalilin dakatar da Yusuf daga aiki da Adewole ya yi ne ya sa babu kyakkawar jituwa tsakain Adewole da Yusuf.
A yanzu haka a kwai rade-radin cewa Yusuf na aikata abinda ya ga dama ne bisa ga sanayyar fadar shugaban kasa.