Za a yi atisayin horas da daliban makarantar sojoji dake Zariya

0

Makarantar sakandare na Sojoji dake Zariya jihar Kaduna (NMS) za ta horas da daliban makarantar daga ranar Juma’a 12 zuwa Asabar 13 ga watan Oktoba a Zariya.

Shugaban makarantar Adekule Adeyemi –Akinyele ya sanar da haka ranar Alhamis a Zariya sannan ya kara da cewa sun shirya wannan horo ne mai taken ‘Exercise Ande’ domin horas da daliban SS2 da SS3 kawai.

Ya ce sun sanar da haka ne saboda mazaunan unguwar Gyellesu ,Anguwan Malam Sule da sauran mazaunan Zariya da su sani kada suji harbe-harbe su tsorata.

Share.

game da Author