Za a fara jigilar masu ziyarar bauta kasar Israela ranar 24 ga watan Nuwamba

0

Shugaban hukumar masu zuwa ziyarar bauta kasar Israela ta kasa Tor Uja ya bayyana cewa hukumar za ta fara jigilar maniyyata zuwa kasar Isra’ila daga ranar 24 ga watan Nuwamba.

Uja ya fadi haka ne a taron horar da ma’aikatan kiwon lafiyan da za su kula da masu ziyara da aka yi a ‘Living Faith’ dake Goshen City a Keffi jihar Nasarawa ranar Litini.

Ya ce tun ba a yau ba hukumar ta tattaunawa da masu ruwa da tsakin a hukumar domin ganin an sami nasara a aiyukkan ziyarar na bana musamman a fannin zabo kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya.

” Hakan zai taimaka mana wajen rage matsalolin rashin lafiya da kuma mace macen masu ziyara da akan samu.

” Bana masu ziyara za su biya kudin tafiya, wurin zama, abinci da dai sauran su a kan Naira 680,000 sannan wadanda ke bukatan ziyartar kasar Roma za su biya Naira 870,000.

A karshe yace sun inganta yin rajistan masu ziyara domin guje wa matsalolin da hukumar ta yi fama da su a shekarun da suka gabata musamman gudu da wasu ke yi a kasar Isra’ila.

Share.

game da Author