Hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na kasa (NPHCDA) ta bayyana cewa an sami karuwar kashi 10 bisa 100 a yi wa yara allurar rigakafi a Najeriya.
NPHCDA ta gano haka ne bisa ga sakamakon binciken da ta gudanar a tsakanin shekarun 2016 zuwa 2018.
Shugaban hukumar Faisal Shuaib ya bayyana haka a taron tattauna matsayin da Najeriya ta kai a yin allurar rigakafi da kawar da cutar shan-inna a Najeriya da aka yi a Abuja.
Shuaib ya bayyana cewa samun wannan sakamakon ya nuna cewa kasar za ta iya rabuwa da cutar shan-inna nan ba da dadewa ba.
” A yanzu dai kasar nan ta yi sama da watanni 24 cur ba a sami sanarwar bullowar cutar shan-inna a ko-ina a fadin kasar ba wanda idan aka ci gaba a haka nan da watanni 11 za ta kai matsayin rabuwa da cutar gabaki daya.
Shuaib ya kara da cewa har yanzu dai fannin yin allurar rigakafin yara na fama da matsalar rashin amincewar iyaye a wasu wuraren.
Ya ce hukumar ta dauki matakan wayar da kan mutane musamman iyaye ta hanyar aikawa da kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya zuwa kauyuka da sauran wuraren da mutane ke kin fito da ya’yan su ayi musu rigakafi.
A karshe wani jami’in kiwon lafiya Oyewale Tomori ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta maida hankali wajen an samu nasarar yi wa yara allurar rigakafin.