‘Yan Sanda sun kama ‘yan Shi’a 400 a Abuja

0

Rundunar ‘yan sandan Abuja ta tabbatar da kama mabiya Shi’a masu zanga-zanga har 400 dangane da hargitsin da ya tashi jiya Talata a cikin babban birnin tarayya, Abuja.

Kwamishinan ‘yan sandan Abuja, Bala Ciroma ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke gabatar da wadanda aka kama din a gaban manema labarai a ranar Talata da yamma.

Ya kara da cewa ana tsare da su inda ake ci gaba da bincike, kuma an kama makaman masu iya yi wa jama’a lahani a hannun su.

Ciroma ya ce an samu bam na kwalba har guda 31 da wasu makamai a hannun wadanda ake tsare da su din.

An kama jami’in agajin su daya dan shekara 23, mai suna Salahudden Ahmad wanda dan asalin Karamar Hukumar Illela ne ta jihar Sokoto.

Kwamishinan ya ce da zarar an kammala bincike, za a tura su kotu domin gurfanar da su a gaban mai shari’a.

Rikici da mabiya Shi’a ya barke tun daga ranar Litinin da safe, inda sojoji suka bude musu wuta a Zuba da kuma Dei-dei, kusa da shigowa garin Abuja.

Sai kuma a hanyar Maraba, inda aka kashe kimanin 22 da kuma na ranar Talata wanda faru a cikin Abuja, a gundumar Wuse II.

An kashe da dama kuma daruruwa sun samu raunuka.

Mabiya Shi’a na zanga-zangar neman a saki jagoransu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, wanda ke tsare tun cikin Disamba, 2015.

Sai da dama kotu na bada umarnin a sake shi, amma gwamnatin tarayya ta yin biris da hukuncin na kotu.

Shekara daya cur da sati biyu kenan sun a gudanar da zanga-zanga a cikin Abuja, banda ranakun Asabar da Lahadi.

Sai dai kuma wannan zanga-zangar, gagarima ce, ta kasa baki yada, domin tuna zagayowar ranar da a kashe Imam Hussaini, jikan Annabi Muhammadu (SAW) a Karbala.

Share.

game da Author