‘Yan bindiga sun harbe ‘yan sandan mobal biyu da farar hula daya a Kaduna

0

Yamutsi ya barke a unguwar Nasarawa a cikin Kaduna yayin da wasu ‘yan bindiga suka bude wuta, har suka kashe ‘yan sandan mobal biyu da farar hula daya.

Farar hular da aka kashe an gano cewa direban kamfanin sarrafa barasa ne na IBBI da ke Kaduna, wanda aka yi kisan a unguwar da masana’antar barasar ta ke.

Haka su ma ‘yan sanda biyun da aka bindige duk su na gadi ne a masana’antar sarrafa basarar, mai suna IBBI.

Harin da bude wutar sun faru ne daidai karfe 5:15 na safiya lokacin da ake shirin fara sallar Asubahi a wani masallaci da ke kusa da masana’antar.

Wani mazaunin unguwar wanda ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa jama’a kowa ya arce yayin da suka ji karar bindiga na tashi.

Sani ya ce su na shirin fara sallah sai suka jin karar bindiga, suna tsammanin ko ‘yan fashi ne.

PREMIUM TIMES ta gano cewa ‘yan sandan guda biyu a nan take suka mutu, shi kuma direban ya mutu a asibitin Saint Gerald.

Akwai wasu ‘yan sandan mobal su biyar da suka ji rauni wadanda su ma ana kula da lafiyar su a asibitin.

Kakakin ‘yan sandan Kaduna, Yakubu Sabo bai dauki waya ba, a lokacin da PREMIUM TIMES ta kira shi domin jin ta bakin sa.

Share.

game da Author