Wasu ‘Yan bindiga sanye da kayan sojoji sun far wa kauyen Abbare, dake karamar hukumar Lau, Jihar Taraba.
Da yake sanar wa manema labarai a garin Abbare, basaraken garin ya bayyana cewa maharan sanye da kayan sojojin sun far wa kauyen ne da misalin karfe 1 na daren Alhamis.
” Suna shigowa kuwa suka hau barin wuta sai da suka hallaka shanu 150. Tun daga wannan lokaci fa masu shanu suka rika daukan wadanda suka ji rauni a harin zuwa kasuwar nama dake Mayu-Belwa da Jalingo domin siyarwa don rage hasara.
Kakakin rundunar ‘Yan sandan jihar Taraba David Misal, ya tabbatar da aukuwar wannan al’amari, sai dai ya ce ko da suka samu labarin abin sun aika da jami’an su domin bin sahun wadanda suka aikata wannan mummunar abu.
Anyi kokarin a ji ta bakin sojojin dake aiki a wannan yanki sai dai ba a dace ba domin kuwa sunce ba a basu daman cewa komai a kai ba.