Wani mutum mai shekara 39, mai Samuel Sheikuma, wanda kafinta ne, ya gabatar da shaida jiya Talata a gaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Sake Fasalin ’Yan Sandan SARS.
Sheikuma wanda dan sintiri ne, ya bayyana yadda wasu ‘yan sandan SARS bakwai suka kashe wata mata mai suna Comport Hembe ta hanyar tunkuda ta kan wayar lantarki, wanda hakan ne ya yi sanadiyyar ajalin ta.
Da ya ke bada shaida a gaban hukumar karkashin Shugaban Hukumar Kare ’Yancin Dan Adam, Tony Ojukwu a Abuja, Sheikuma ya ce likitan da aka kai Hembe asibitin sa ya shaida musu cewa matar ta mutu ne sakamakon karfin wutar lantarkin da ta ja ta.
Ya ce al’amarin ya faru ne a ranar 18 Ga Yuni, 2018, inda wasu SARS su bakwai suka kai farmaki a cikin wani gida, suka rika kutsawa cikin dakuna, har suka samu matar kwance tare da saurayin ta mai suna Mr. Dogo, suka hankado ta waje kusan tsirara.
Ya ci gaba da cewa sun kwace wayar matar saboda kawai ta ki ba su kudi. Sun kuma daure ta da ankwa, saboda da farko ta ki yarda a kama ta.
“Daga nan suka fara tankiya, sai suka fara dukan ta, kuma suka tura ta a jikin kofar gidan, inda nan take sai wayar lantarki ta rike matar, ta rika jijjiga.”
“Daya daga cikin SARS ya yi kokarin ciccibar ta daga jikin kofar, amma da ya ji karfin lantarki ne ya rike ta, sai ya yi baya.
‘Daga nan sai hudu daga cikin SARS bakwai din suka tsere, suka bar uku. Wadannan ukun ne suka saka ta a mota zuwa asibitin Gwarimpa, bayan sun yi amfani da sanda sun bambare ta daga jikin inda wutar lantarki ta rike ta.
“Matar ta mutu bayan an kai ta asibiti.”
A lokacin da mai gabatar da kara na ‘yan sanda, James Idachaba ya tambaye shi alakar sa da gidan da al’amarin ya faru, ya ce shi dan sintiri ne, na bigilanti, wanda ke kula da unguwar.
Ya kara da cewa shi dan sintiri ne a unguwar Mabushi, inda abin ya faru. Kuma daga SARS sun saba zuwa gidan ba tare su na sanar da DOP na shiyyar ba.
Ya kara da cewa wajen 12 na dare abin ya faru, domin ya ji lokacin da matar ke cewa akwai karfin lantarki a kofar, kada su tura ta fa.
Tony Ojukwu ya daga sauraren wannan bayar da shaida zuwa yau Laraba, 24 Ga Oktoba.
Discussion about this post