Yadda rashin wutan lantarki ke gurgunta ayyukan yin allurar rigakafi a Abuja

0

Cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko dake kananan hukumomin Gwagwalada da Kuje sun koka kan fama da suke yi da rashin wutar lantarki a asibitocin su.

Bayan haka asibitocin sun bayyana wa wakilan PREMIUM TIMES da suka ziyar ce su cewa akwai kuma matsalar dakunan ajiyar magunguna da suke fama da su da ya hada da wuraren ajiyar maganin rigakafin cututtuka.

Cibiyoyin da PREMIUM TIMES ta zazzagaya sun hada da na kananan hukumomin Tungan Maje, Abaji, Kuje da na cikin garin Gwagwalada.

A kwanakin baya gwamnatin tarayya ta yi alkawarin shawo kan wasu matsalolin dake ci wa yin allurar rigakafi tuwo a kwarya kamar su rashin isassun kudade, yin zagon kasa da ake yi wa shirin da kamar kuma gwamnati ba ta gane cewa rashin wutan lantarki da ingantaccen dakunan ajiya na cikin wadannan matsaloli da ake fama da su a cibiyoyin kiwon lafiya na wadannan yankuna.

John Awodi ma’aikacin cibiyar kiwon lafiyar dake Tungan Maje ya bayyana cewa tun da suka sami dakin ajiyar maganin allurar rigakafi dake amfani da hasken rana matsalolin su ya ragu.

” Kafin mu sami wannan na’urar wuta na Sola, na fita ne zuwa cikin garin Gwagwalada domin yin jigilar magungunan rigakafin da za mu bukata a duk ranar. Sannan a dalilin wannan wuta da muke samu yanzu, mun samu raguwa matuka wajen jira da mata ke yi a asibiti, sannan har mukan taimaka wa asibitocin dake garuruwan Zuba, Anaagada, Shegwegwu, Kpakuru da inda za su ajiye maganin rigakafin su.

Ma’aikatan cibiyar kiwon lafiyar dake Abaji sun bayyana cewa basu da wurin ajiyar maganin rigakafi sai dai sukan karbo ne daga wani asibiti dake kusa sa su.” Da ace zamu samu wurin ajiya a namu asibitin da za mu fi samun sauki wajen ayyukan mu” Inji Ma’aikaciya, Hassana Mohammed.

A Gwagwalada kuwa ma’aikata sun bayyana cewa na’urori Sola da ke basu wuta da inda suke ajiya maganin na gab su daina aiki.

” Muna da wurin ajiyan dake amfani da wutan lantarki sannan da na hasken rana amma duk sun lalace.

A Karamar hukumar Kuje kuwa gaba daya ma ba su aiki ne kwata-kwata.Sukan yi amfani da Janareto ne idan dole sai sun yi amfani da magani.

” A lissafe mukan samar wa yara ‘yan kasa da shekaru biyar 56,609, yara ‘yan shekara kasa da daya 11,322 sannan da mata masu ciki 14,152 magungunan rigakafi a mazabu 10 dake karamar hukumar.

A karshe shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na babbar birnin tarayya Abuja (FCT PHC) Rilwanu Mohammed ya bayyana cewa hukumar su bata da ikon daukan mataki game da matsalolin da cibiyoyin kiwon lafiyar yankin ke fama da su domin har yanzu majalisar dokoki na kasa bata kammala tattance dokar da zai basu ikon yin haka.

Mohammed yace duk da haka hukumar na shirin samar wa asibitocin da suka fi bukata na’urar Sola da dakunan ajiyar magungunan domin samun nasara a aikin da suka a sa gaba.

Share.

game da Author