Shugaban Kungiyar IPOB, masu neman kafa kasar Biafra a Najeriya, Nnamdi Kanu, ya yi magana a kan yadda ya tsere daga Najeriya.
A cikin wata hira da aka yi da shi a wani gidan talbijin na Isra’ila, inda ya ke gudun hijira, ya bayyana cewa ‘yan uwan sa ne suka taimaka masa ya sulale.
“A ranar sojojin Najeriya sun dira gida na, da nufin su kashe ni. Domin sun kashe mutane har 28 a cikin gidan.”
“Dangi na suka yi sauri suka dauke ni daga cikin gidan, suka fitar da ni daga Najarriya. A yanzu hankali na kwance ya ke, domin ina zaune a kasar na fi jin cewa a duk duniya nan ne zan fi samu a kare min rai na da lafiya ta.”
Kanu wanda baya ga dan Najeriya ne, kuma ya na katin zama dan kasar Birtaniya, ya ce zai fi so a ce ya na Ingila a yanzu haka, amma kuma a can hankalin sa ba zai kwanta ba, kamar a ce ya na cikin kasar Isra’ila.
A cikin hirar, Kanu ya danganta ‘yan kungiyar sa ta IPOB da cewa duk mabiya addinin Yuhudanci ne, da ya ce kuma akwai kabilar Igbo a warwatse a duniya kusan milyan 70.
Discussion about this post