Yadda na shafe kwana biyu a hannun masu garkuwa da mutane – Gambo

0

Wata budurwa mai shekaru sha shida, mai suna Gambo, ta bayyana yadda ta shafe kwanaki biyu a hannun wadanda suka sace ta.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda aka sace Gambo a ranar 10 Ga Oktoba, a Kwanar Soja, cikin Karamar Hukumar Jos ta Arewa, a jihar Filato.

A kokarin da wani soja ya yi domin kubutar da ita a lokacin sai ya rasa ran sa, bayan da barayin suka bindige shi.

Kakakin ‘yan sandan jihar Tyopev Terna ya tabbatar wa Premium Times sace budurwar a waccan ranar.
Yayin da aka tambayi ‘yan sandan a jiya Alhamis ko su na da masaniyar sako Gambo, sun ce kwarai kuwa sun samu labarin sako ta.

PREMIUM TIMES ta ji daga bakin mahaifin Gambo mai suna Idris Gambo cewa shi da matar sa kuma mahaifiyar Gambo din ne kawai suka je suka samu masu garkuwa da ita kafin a sako ta.

Jiya Alhamis ne kuma Gambo ta shaida wa PREMIUM TIMES halin da ta tsinci kan ta a cikin kwana ki biyun da ta yi a hannun wadanda suka yi gaskuwa da ita.

“Ina zaune cikin gida a ranar 9 Ga Oktoba, da misalin karfe 7:30 na dare, sai kawai na ji karar harbin bindiga a kofar gidan mu. Ba a jima ba sai wasu mutane sanye da kayan sojoji suka kutso kai a cikin dakin mahaifiyar mu, suka umarce mu kowa ya kwanta kasa. Sai suka fara tambayar ina kudi? Ku ba mu kudi.”

Ni kuma nace musu babu kudi.

“Daga nan sai suka tambaye ni ko ni ce Hajiya? Na ce musu a’a. Sai suka shiga dakin mahaifi na suka iske mahaifiya ta a can. Suka gaura mata mari, kuma suka tambaye ta kudi. Nan dai suka dauke dukkan kudaden da mahaifiya ta ke da su a gidan.

“Sun yi niyyar tafiya da mu duka ukun, amma dai suka yi nasarar tafiya da ni kadai. Mun yi doguwar tafiya a cikin daji tsawon awanni da yawa. A karshe muka tsaya, muka wayi gari a bayan Kwalejin ‘Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya da ke Jos.

“Gari na wayewa da sassafe kuma sai muka nausa cikin wani daji a kan hanyar Jos zuwa Bauchi. A can muka tsaya, suka kira lambar wayar mahaifiya ta, suka ce sai su kai musu naira miliyan 10. Ita kuma ta ce ba ta da wadannan kudaden.

“Ta yi ta rokon su, a karshe dai suka ce mata ta zo nan inda za ta same mu. Bayan ta zo da sassafe, ban san abin da ta ba su ba, amma dai ta ba su wani abu, daga nan sai suka kyale ni na bi mahaifiya ta muka tafi gida.

“Ba karamin bala’i na gani ba, kuma bazan yi fatan sake samun kai na cikin wannan abu ba. Na sha tafiya a kasa tsawon kilomita da yawa. Ban yi tsammanin zan iya yin wannan doguwar tafiya ba.”

Share.

game da Author