Abu dai kamar almara sai ga shi an nuno gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje yana karbar cin hancin bandir-badir din daloli ya karkacewa ya na loda wa a aljuhan babban rigar sa.
Jaridar Daily Nigerian ne ta bankado wannan badakala inda ta saki wani bidiyo dake nuna Ganduje karara yana buga harka abin sa.
Duk da cewa akwai tabbacin aukuwar wannan harkalla bisa ga bidiyon da jaridar ta fitar, gwamnatin jihar Kano ta fito karara ta barranta kanta daga wannan badakala.
Sai dai kuma mawallafin jaridar Daily Nigerian, Ja’afar Ja’afar da yanzu haka yana boya bisa ga tsoron farmaki da ake neman kai masa ya tabbatar da aukuwar wannan al’amari.
Ja’afar ya ce ba tun yanzu ya fara bibiyar gwamnan ba domin bankado ire-iren harkallar da yake tafkawa a kwangiloli da gwamnati ke badawa a jihar Kano.
Ya ce an dade ana shirya masa gadar zare inda a karshe ya fada.
Wani daga cikin ‘yan kwangilar da ya nemi a boye sunan sa ya fadi cewa tabbas shine ya rika mika wa Ganduje wadannan kudade kuma ya tona asirin sa ne don a gyara.
” Ni ban tona wa Ganduje asiri don son rai. Idan da haka ne da na yi amfani da bidiyon da na dauka muna biyan sa cin hanci sun fi 10 wajen azurta kaina ko kuma tilasta masa ya biya kamfanin mu kudaden da muke bin su.
” Ina da yakinin cewa idan ana fallasa jami’an gwamnati haka Najeriya za ta gyaru.
Gwamnatin jihar Kano ta karyata wannan bidiyo sannan ta ce tabbas za tu gudanar da bincike akai da idan ya kai ga a shiga kotu ne ma za a shiga don a wanke gwamna Ganduje.
Discussion about this post