Jakadar kasa Amurka ta bayyana cewa USAID za ta tallafa wa Najeriya da dala miliyan 65 domin ci gaban kasa Najeriya.
Jami’in gwamnatin Amurka Stephen Haykin ya sanar da haka a Abuja ranar Talata inda ya kara da cewa wannan tallafin kari ne bisa ga yarjejeniyyar ba da tallafi da Amurka ta yi wa Najeriya.
Idan ba a manta ba a 2015 ne kasar Amurka ta amince ta tallafa wa Najeriya da dala biliyan 2.45 wanda za a yi amfani da su wajen samar wa Najeriya ababen more rayuwa da samar da tsaro na tsawon shekaru biyar.
Wannnan kari da aka samu na dala miliyan 65 na nuna cewa zuwa yanzu an iya samar da dala biliyan 1.17 wa kasa Najeriya cikin tallafin da aka yi alakwarin bata na dalar Amurka biliyan 2.15.
Haykin ya kara da cewa dala miliyan 59.33 daga cikin wannan kudade PEPFAR za ta yi amfani da su wajen tallafa wa masu fama da cutar kanjamau.
” Za kuma muyi amfani da dala miliyan 4.67 domin karfafa aiyukkan gwamnatocin jihohi da kananan hukumomin a arewa maso gabashin Najyariya wajen samar wa mutanen yankin ababen more rayuwa.
” Sannan za mu yi amfani da dala miliyan 1.5 domin dakile yawa-yawan rikice-rikice dake tasowa a kasar nan.