Wata likitar Yara kuma ma’aikaciyar asibitin jami’ar Legas (LUTH) Okiemute Olibamoyo ta bayyana cewa yi wa yaro dure ko kuma tursasa masa ya ci abinci na da matukar illa ga lafiyar sa.
Olibamoyo ta fadi haka ne da take hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Legas.
Ta ce Illar tursasa wa yaro cin abinci na iya sa yaron ya tsani abinci, yaro na iya shakewa sannan garin kokawar bashi abinci ana iya ji masa rauni.
Olibamoyo ta bayyana cewa mafi yawan iyaye matan dake aikata haka wa ‘ya’yan su na yin hakan ne cikin rashin sanin wadannan illolin dake tattare da tursasa wa yara cin abinci.
” Wasu kuma na da canfin cewa tun da iyayen su sun yi musu haka da suke kanana kuma suka rayu dole ‘ya’yan su bi wannan hanya da suka biyo.
Ta ce kamata ya yi iyaye mata su kula da irin abincin da ‘ya’yan su ke son ci ko kuma su canza yadda suke dafa abincin su.
” A wani lokacin sai ka ga yaro ya ki abincin uwar sa amma ya je yana cin abinci a wani wurin wanda hakan ke nuna cewa akwai abin da mahaifiyar sa ke saka wa a cikin abincin da shi baya so.
Olibamoyo ta kuma ce mata su ringa shayar da ‘ya’yan su ruwan nono yadda ya kamata na tsawon watanni shida akalla kafin a fara bashi abinci.
Sannan za a iya samun bayyanan abincin da ya kamata uwa ta ba danta bayan ta shayar da shi na tsawon watanni shida a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko dake kusa da su.