Tsohon Kwamishinan Jigawa ya koma APC da magoya bayan sa 10,000 daga PDP

0

Tsohon kwamishinan shari’a a lokacin mulkin PDP na Sule Lamido Yakubu Ruba ya canja sheka daga jam’iyyar sa ta PDP zuwa jam’iyyar APC.

Ruba ya bayyana cewa ya yanke haka ne bayan doguwar nazari da yayi da kuma irin fandarewar da jam’iyyar tayi a jihar.

” Na isa in yanke wa kai na shawarar inda na nufa a siyasance. Na gaji da hayaniyar PDP duk da na bauta wa jam’iyyar yadda ya kamata amma yanzu na ga cewa ba zan iya cimma burina a siyasance ba dole in canja sheka.

Tare da Ruba magoya bayan jam’iyyar PDP 10,000 suka canja sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Share.

game da Author