Tsare Dan Majalisar Tarayya na neman hada Majalisa da Sufeto Janar Idris

0

Majalisar Tarayya ta umarci Sufeto Janar Ibrahim Idris ya bayyana a gaban ta, dangane da tsare daya daga cikin mambobin ta, Abubakar Lado da rundunar SARS ta yi.

Sun umarce shi da ya bayyana ce bayan zaman ta na biyu daga dawowa hutun watanni biyu da majalisar ta yi.

Lado wanda mamba ne daga jihar Neja kuma dan jam’iyyar APC, da ke wakiltar Gurara/Suleja/Tafa, ya na hannun jami’an SARS ne, kuma an nemi a sake shi cikin awa 12 bayan umarnin da majalisar ta bayar.

Dan Majalisar Tony Okechukwu daga jihar Anambra, kuma dan PDP ne ya fara yin magana dangane da tsarewar da aka yi wa Lado, tare da jan hankalin majalisa da Kakakin ta, Yakubu Dogara cewa a fa yi wani abu.

Okechukwu y ace an tsare dan majalisar kwanaki uku ya zuwa jiya Laraba, kuma tsarewar ta sa na da nasaba ne da sabanin zaben takarar fidda gwanin APC a jihar Neja.

Dukkan sauran wadanda suka yi jawabi, sun goyi bayan Okechukwu, wanda hakan ya sa kakakin majalisa yin amfani da ra’ayin masu rinjaye kan a gaggauta sakin Lado, kuma Sufeto Janar Idris ya bayyana a gaban majalisa.

Tun farkoinji shi, sai da Lado ya sanar wa jami’an tsaro cewa ana neman a tada rikici a zaben fidda gwanin APC din.

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN ya ruwaito cewa Lado na takarar kujerar majalisar tarayya ce tare da shugaban karamar hukumar Suleja, Abdullahi Maje.

Share.

game da Author