A yau Laraba ne daru ya barke a majalisar Dattawa tsakanin sanatocin jam’iyyar APC da na PDP bayan shugaban majalisar ya ki amincewa Sanata Godswil Akpabio da yi magana a zauren majalisar.
Saraki ya nemi Akpabio da ya koma wajen zaman sa kafin ya bashi damar fadin abin da ya ke so ya fadi ko kuma ya hakura da abinda ya ke so ya fadi.
A dalilin haka majalisa ta yamuste inda kowa ya ja daga.
Kafin haka shugaban masu rinjaye na majalisar Ahmed Lawan ya nemi Saraki ya amince wa Akpabio da ya yi magana a zauren majalisar amma hakan bai yiwu ba.
Idan ba a manta ba Akpabio, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, ya garzaya Landan inda Shugaba Muhammadu Buhari ke zaman hutu ya je ya yi mubayi’ar komawa jam’iyyar APC daga PDP.
Bayan dawowar sa Najeriya kuma, Akpabio ya ziyarci jagoran APC, Bola Ahmed Tinubu.
Ya shiga APC dauke da shirgin nauyin zargin harkallar danne wasu biliyoyin kudade.
Hawan Buhari mulki ke da wuya a cikin 2015, Akpabio na daya daga cikin wadanda yaki da cin hanci da wawurar kudade ya fara yi wa dirar mikiya.