TONON SILILI: Yadda Ministan Fetur, Kachikwu cusa karya a cikin shaidar digirin sa

0

Karamin Ministan Fetur Ibe Kachikuwu ya cukuikuya karya a cikin satifiket din digirin sa na fannin shari’a, inda ya yi ikirarin cewa ya samu digiri mai Daraja ta Daya (First Class), alhali karya ya ke yi.

Kachikwu ya kantara wannan karya ce kimanin shekaru biyu da suka gabata, yayin da ya ke jawabi a wurin bikin cikar Cocin Commonwealth of Zion Assembly (COZA), shekaru 17 da kafawa, a Abuja.

An nuno shi a cikin wani bidiyo da yanzu haka aka watsa a youtube ya na wannan jawabi a ranar 17 Ga Fabrairu, 2016, inda Kachikwu ya kantara wannan karya a gaban dimbin jama’a, a cikin cocin COZA.

Yayin da dadin zance ya kwashe shi, Kachikwu ya ci gaba da bai wa masu sauraro irin gaganiyar tarihin rayuwar sa da hakilon da ya sha wajen neman ilmi.

“Tun farko ni na so zama babban likita ne, to da na shaida wa mahaifi na cewa zan karanta aikin lauya, sai ya garzayo daga garin Ife ya same ni, ya ce don me zan karanci fannin lauya?

A cikin bidiyon dai, Kachikwu ya ci gaba da cewa, yayin da shaida wa mahaifin sa salili, sai kawai ya dauki jakar sa, ya fice daga makarantar koyon aikin likita, ya tafi ta koyon aikin lauya da shari’a a Jami’ar Nsukka.

“Na je shiga makarantar aikin lauya, na zama dalibin da ya dukkan sauran daliban kokari, har na samu Digiri mai Daraja ta Daya.” Inji Kachukwu.

Kachikwu ya ci gaba da cewa da ya je Jami’ar Harvard a Amurka, Jami’ar da ta fi saura shahara, ya zama dalibin da ya fi sauran dalibai hazaka a digirin sa biyu a fannin sanin shari’ar makamashi da albarkatun man fetur. Sannan kuma a Makarantar Koyon Aikin Shari’a ko Lauya, shi ne ya samu Digiri mai Daraja ta Daya.

Har ila yau, Kachikwu ya ce tun da ya bar Jami’ar Harvard da ke Amurka, har yau ba a sake samun dalibin da ya kai shi kokari a fannin da ya yi kwas ba.

KARAIRAYIN KACHIKWU: BA YAU NE FARAU BA

*Baya ga karyar samun digiri mai daraja ta daya da kuma furta cewa shi ne ya fi sauran daliban jami’ar Harvard hazaka , wadda Minista Kachikwu ya shirga a gaban dubban jama’a a cikin coci, ya kuma cusa wannan karya a cikin a cikin bayanan tarihin rayuwar sa da bayanan dimbin ilmin da ya ke da shi, wanda aka buga a cikin shafin intanet na Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur ta Tarayya.

Dukkan karairayin da ya kantara a gaban jama’a a cikin coci, su na can a rubuce a shafin intanet na Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur, duk an maka su a can.

*A shafin tattara bayanan jama’a na intanet na duniya mai suna Wikipedia ma, dukkan wadannan karairayi na Kachikuwu na can a rubuce.

KO KACHIKWU YA FI SAURAN DALIBAN HARVARD KOKARI?

Domin tabbatar da gaskiyar abinda ministan ya yi ikirarin ya samu na mafificin dalibin da ya fi saura hazikanci a Jami’ar Harvard ta Amurka, PREMIUM TIMES ta aika wa jami’ar da wasikar neman karin bayani, kuma a na zaman jiran amsa.

YADDA PREMIUM TIMES TA GANO KARYAR KACHIKWU

PREMIUM TIMES ta mallaki takardun karatun Minista Kachikwu na gaskiya, inda ta gano cewa ya shiga Jami’ar Nsukka cikin 1974, inda ya shafe shekaru hudu ya yi digiri a fannin lauya.

Kwalin digirin Kachikwu wanda ke dauke da sa hannun Shugaban Jami’ar na lokacin, ya nuna cewa Kachikwu ya samu Digiri mai Daraja ta Biyu ne, ba Mai Daraja ta Daya kamar yadda ya ke barazanar ya samu ba.

KACHIKWU SARKIN KARYA

Ba wannan ne karon farko da wannan jarida ta taba buga bayanan da ko dai Kachikwu ya kantara ba, ko kuma inda ya yi baki-biyu.

*Kachikwu ya taba shirga wa Babban Manajan Daraktan Kamfanin Mai na NNPC, Maikanti Baru karya cewa ya bayar da wata kwangila a asirce ta naira bilyan 885 domin gina bututun mai daga Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano. A ranar 23 Ga Disamba, 2017 ne PREMIUM TIMES ta gano cewa karya Kachikwu ya shirga wa Maikanti Baru.

*Sai wata karya da Kachikwu ya kara shirgawa, inda ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannun amincewa a kan wannan kwangila, bayan yin biris da jin ta bakin Hukumar Gudanarwar NNPC da Buhari din ya yi.

*Kachikwu da ya ce Buhari ya sa wa kwangilar hannu tun lokacin da Maikanti Baru ya kai masa, sai kuma ga shi ya dauki kwafen takardun kwagilar ya je da su taro Majalisar Ministoci a gaban Buhari, a ranar 13 Ga Disamba, ya na neman a sa wa kwangilar hannu.

*Takardun bin ba’asin kwangila dalla-dalla da Kachikwu ya kai wa Buhari domin a sa hannu, sun tabbatar da cewa a cikin watan Agusta, 2017 da kuma ranar 6 Ga Disamba aka rattaba su kafin a gabatar wa Shugaba Buhari. Alhali kuma Kachikwu ya shirga wa Maikanti Baru karya cewa tun a cikin watan Yuni shi Baru din ya kai kwangilar aka sa mata hannu.

Share.

game da Author