Wani sabon bidiyo ya shiga duniyar yanar gizo, inda aka nuno Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje na karbar damman daloli ya na cusawa cikin aljifan kaftanin sa.
Sai dai kuma Babban-Editan Daily Nigerian, wanda jaridar sa ce ta saki wadancan bidiyo biyu na baya, ya musanta cewa shi ne ya saki bidiyon.
Jaridar PRNigeria ta tabbatar da cewa Jaafar ya damka dukkan kwafe-kwafen bidiyon da aka nuno Ganduje na karbar kudaden a hannun ‘yan Majalisar Jihar Jihar Kano, a lokacin da ya amsa gayyatar da suka yi masa cikin makon da ya gabata.
“Ai ni na yi rantsuwa da Alkur’ani a lokacin da na gabatar wa kwamitin majalisar jihar Kano kwafen bidiyon. Don haka bai yiwuwa kuma na kasance wanda ya saki wannan bidiyon da ke yawo a soshiyal midiya a yau. Don haka Daily Nigerian ba ta sake sakin wani bidiyo ba, tun bayan da na je gaban kwamitin bincike a Kano.” Inji Jaafar.
Bidiyon da ke yawo a yanzu, ya nuno Ganduje na karbar rashawa daga hannun ‘yan kwangila, kuma ana lissafa sunayen wadanda suka bayar da kudaden rashawar ga Gwamna Ganduje.
A bidiyon har da sunan rana da kwanan watan da aka karbi kudaden, wadanda aka nuno Ganduje na karba, bayan an yi masa bayani dalla-dalla na wadanda suka bayar da kudaden, shi kuma ya na zurawa aljifan sa.
A karshen bidiyon dai wanda ke mika masa kudin har ban-kwana ya yi wa Ganduje, abin da ke nuni da cewa a lokacin gwamnan ya na cikin hanzarin yin wata tafiya zai bar Kano.
Akwai ma inda bayan an damka masa wani damen daloli kuma an yi masa bayanin ko wane dan kwangila ne ya bayar da ita, Ganduje yay i tambayar shin ya kuwa fara aikin? Mai bayar da kudin ya amsa da cewa aiki ma ya yi nisa.
[youtube https://www.youtube.com/watch?v=zs9Qm4Ub1M8&w=560&h=315]
Akwai kuma sunan wani dan kwangila da aka kira, aka shaida wa Ganduje cewa shi kuma bai samu ‘‘kai kudin na sa jiya ba, saboda babu cikon dala 100,000. Sai yau ya kawo.”
Har yanzu dai ana tunin wa zai saki bidiyon, domin tun bayan da Jaafar ya ziyarci kwamitin bincike, kwafe-kwafe na bidiyon sun shiga hannun mutane da dama, tun daga mambobin kwamitin bincike, jami’an tsaro da wasu masu ruwa da tsaki da batun ya shafa.