Hukumar Kula da Kadarorin Kadarori ta Kasa (AMCON), ta fara fallasa sunayen wasu hamshakan ‘yan Najeriya masu taurin bashin da suka ki zama tare da hukumar domin su warware ko su sauke nauyin da ke kan su.
Jadawalin sunayen mutanen tare da sunayen kamfanonin su, har su 105, an buga shi ne jiya Litinin, kuma AMCON ta ce za ta shigo da hukumomin da suka dace a cikin wannan kiki-kakar, domin a tabbatar wadanda aka buga sunayen na su sun biya basussukan da ke kan su.
Idan ba a manta ba, Manajan Darakta na AMCON, Ahmed Kuru, ya yi barazana tun cikin watan Yuli cewa zai buga sunayen sunayen kamfanoni da masu kamfanonin, wadanda suka ki biyan dimbin bashin da aka bin su.
Na farko a jerin sunayen shi ne Ifeanyi Ubah, mai Capital Oil and Gas Industries Limited, wanda ake bin kamfanin sa bashin naira biliyan 115.
Sai kuma Jimoh Ibrahim mai NICON Investment Limited, naira biliyan 59. Shi kuma Wale Babalakin mai kamfanin Bi-Courtney, ana bin kamfanin sa bashin naira biliyan 40.
A ciki har da sunan Barth Enaji, tsohon ministan makamashi, wanda ake bin kamfanin sa Geometric Power Industries bashin naira biliyan N29.
Akwai ma inda sunan Babalakin ya sake fitowa, inda ake bin wani kamfanin sa bashin naira bilyan 29.
Sunan tsohon gwamnan jihar Enugu, Chimaroke Nnamani ya fito, inda ake bin kamfanin sa mai suna Iorna Global Resources da wasu gungun kamfanoni bashin naira biliyan 42.
Ana bin kamfanin Buruji Kashamu bashin naira biliyan 13.015, sai kuma kamfanin Joshua Dariya, tsohon gwamnan Filato da ke daure zai shafi shekara 14, shi ma ana bin kamfanin sa bashin naira biliyan 6.8.
sai dai kuma Babalakin ya karyata cewa ana bin kamfanin sa na Bi-Courtney kudi. Cikin wata wasika da ya aika wa PREMIUMTIMES, ya ce AMCON ba ta bin Bi-Courtney bashin ko sisi.