Hukumar EFCC ta maida raddi dangane da karar da wani dan asalin jihar Edo ya shigar kotu, ya na kalubalantar EFCC saboda ya nemi ta binciki tsohon gwamnan jihar, Adams Oshiomhole, amma hukumar ta kau da kai a kan sa.
Oshiomhole wanda ya yi gwamnan jihar Edo daga 2008 zuwa 2016, shi ne shugaban jam’iyyar APC na kasa, jam’iyyar da ke kan mulki a yanzu.
A karar da ya shigar, Mista Ochie ya nemi kotu ta tilasta wa EFCC bincikar Oshimhole dangane da zargin harkalla da wawurar makudan kudade da ya yi masa, kuma ya gabatar da takardun shaidar cin kudaden a gaban EFCC, amma hukumar ta kau da kan ta.
Wannan rokon da ya yi wa kotun ne ya sa ita Babbar Kotun Tarayya ta Abuja din ta aza ranar Talatar da ta wuce a matsayin ranar da za a fara sauraren kara, kuma aka ce an aika wa kowace bangare sammacin sanarwa.
Yayin da lauyan Oshimhole ya bayyana a kotu a ranar Talatar da ta gabata, babu wani lauya daga bangaren EFCC da ya je kotun.
A kokarin kare Oshiomhole da lauya ya yi tun da fari, ya yi kokarin hana a binciki shi shugaban APC din na kasa baki daya, a bisa dalilin cewa wa’adin caje-cajen da ake yi wa wanda ya ke karewa din ya wuce.
Sai dai kuma a na ta bangaren, EFCC ta ce ta ki zuwa kotun ne saboda wanda ya shigar da karar bai aika mata bayanan abin da kotun ta zartas ba.
A baya kotu ta tilasta wa EFCC cewa tilas ta karbi takardun korafin da aka kai mata kan zargin wawurar kudaden da ake yi wa Oshimhole ta bincike shi kuma ta gurfanar da shi.
Amma sai Oshimhole ya kai kara wata kotun inda ya nemi a hana EFCC bincikar sa din da waccan kotun ta ce sai an yi.
Kakakin EFCC Wilson Uwejaren ya nuna damuwar sa kan yadda lauyan mai shigar da kara, West Idahosa ya yi wa kotu ikirarin cewa ya aika wa EFCC bayanan da ya kamata ya aika mata.
Ya ce da an aika wa EFCC da kwafen bayanan, da wakilin ta ya bayyana a kotun.
Tun bayan saukar Oshiomhole daga gwamnan jihar Edo ne ake ta bin EFCC da kwafen korafe-korafen harkallar kudaden da ake zargin ya yi, amma ba ta yi komai a kai ba.
Wannan ne ya sa mai korafin ya garzaya kotu, domin kotu ta tilasta wa EFCC binciken shugaban jam’iyyar APC na kasa din a yanzu.