Taron kaddamar da littafin Jonathan zai hada Buhari, Obasanjo, Atiku da T.Y Danjuma wuri daya

0

Shugaba Muhammadu Buhari, tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, na daga cikin manyan bakin da ake kyautata zaton za su halarci taron kaddamar da littafin tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan.
Littafin mai suna ‘My Transitin Hours’, ya tabo batutuwan da suka faru ne a lokutan da Jonathan ke kokarin shirya mika mulki ga Muhammadu Buhari, bayan ya fadi zaben 2015.

Za a kaddamar da littafin ne a ranar 20 Ga Nuwamba, ranar da ta yi daidai da ranar haihuwar Jonathan.

Buhari zai kasance Babban Bako na Musamman, Obasanjo kuma Shugaban Taro, yayin da Atiku kuma Bako na Musamman.

Sauran manyan bakin da za su halarci aron sun hada da tsohon Babban Mai Shari’a na Kasa, Salihu Ibrahim, wanda zai yi sharhi a kan littafin, sai T.Y Danjuma da zai zama Mai Gabatar da Littafi, da kuma Gwamnan Jihar Rivers, Seriake Dickon a matsayin Mai Masaukin Baki.

Ana kuma sa ran halartar wasu shugabannin Afrika na yanzu da wadanda suka taba yin mulki, ciki har da tsohon Shugaban Kasar Ghana, John Mahama.

Share.

game da Author