TAMBAYA: Mene ne hukuncin rasa sallar Juma’a, Tare Da Imam Bello Mai-Iyali
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Sallah itace mafi girman Ibadar da Allah ya shar’antawa bayinsa. Sabo da girmanta Allah ya sanyata rukuni na biyu daga cikin rukunnan musulunci kunma sabo da muhimmancinta, annabi ya tafi sama domin karbota. Allah ya tattali lada mai yawa ga wanda ya tsareta kamar yadda ya tanaji azaba mai girma ga wanda ya tozartar da ita.
Sallar Juma’a tanada fifiko da girman daraja, Allah ya tara al-hairi mai dunbin yawa a cikinta kuma ya zabeta a matsayen idi ga musulmai, suna taruwa, su tattauna kuma su sada zumunci da yada sakon musulunci.
Lalle sallar juma’a wajibi ne ga dukkan musulmi namiji, baligi, mazauni, lafiyayye. Duk wanda yabarta, to ya tafka hasara kuma yayi babban zunubi. Hadisi ya inganta cewa duk mutumin da ya bar juma’a sau uku to, an rubutashi daga cikin munafukai. A wata riwayar kuwa, to ya warware musuluncinsa. Lalle mai sakaci da sallar juma’a yana cikin hadari mai girma, ana toshe zuciyarsa, ana nisantashi daga rahama, zai dawwama acikin zunubi da fushin Allah. Ba’a karban shaidan mai barin juma’a. A mazhabar shafi’iyya kuwa, ana kashe dukk mutumin da yabar juma’a da gangan.
Duk bawan da ya bar juma’a bada uzuri ba, yayi gaggawan tuba zuwa ga Allah, kuma ya sallaceta a matsayin Azzahar.
Allah shi ne mafi sani.