Sojojin Najeriya ba su maular abinci ya Arewa-maso-Gabas – Gwamnatin Najeriya

0

Gwamnatin Tarayya ta karyata kuma ta yi watsi da wani rahoto da wata kafar kada labarai ta ‘online’ ta wallafa cewa sojojin Najeriya masu yaki da Boko Haram su na maular abinci a yankin Arewa-maso-Gabas.

Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ne ya bayyana wannan zargi a matsayin irin labarai na bogi da kirkirar karyar da wasu kafafen yada labarai na ‘online’ ke yi.

Ministan ya ce sakamakon irin nauyin barazanar da irin wannan labari kan iya haifarwa, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a bincika domin a tabbatar da gaskiyar labarin.

Ya kara da cewa to yanzu dai an kammala bincike, kuma dalili kenan ministan ya ce ta kira taron ‘yan jarida domin ya shaida musu sakamakon da binciken ya nuna.

“A takaice dai bincike ya tabbatar da cewa babu inda aka taba samun wani korafin barin sojojin Najeriya da yunwa, har a ce sun je su na maular abinci a fadin Arewa-maso-Gabas, musamman ma a cikin bataliyar da rahoton ya bada misali a cikin rahoton da aka buga na zarfgin.

“Sannan kuma babu inda aka rika yanke wa sojoji alawus-alawus din su ko kuma yi musu tsallaken wasu watanni ba a biya su ba. Kuma babu inda suke da karancin wurin kwanciya ko kayan shimfida da na amfanin yau da kullum. Duk karya ce rahoton jaridar, kuma zargi ne marar tushe, marar gaskiya.” Inji Lai.

Ya yi mamakin yadda za a ce gwamnatin tarayya wai za ta bar sojoji a cikin yunwa ko karancin abinci. Batun kudaden alawus kuma ya ce kowa kai tsaye ake tura masa na sa alawus din a cikin asusun ajiyar sa na bankin da ya ke adana kudaden sa.

Lai ya ce kuma kai-tsaye daga hedikwatar sojoji ta kasa ake tura wa kowa kudaden sa, ba sai sun bi ta hannun wani dan aike ba.

Share.

game da Author