Tabbas an gudu ba a tsira ba a hannun dattijai,shugaba Buhari da Atiku Abubakar duk sun haura shekara 70 amma sun bawa wadanda ake gani kamar sune matasan ‘yan siyasa ruwa.
Ba don kada nayi ta mahaukaci ba,da sai nace ban taba ganin siyasa mai sabani ba irin ta wannan lokacin. Misali, duk wanda ya dauka da zafi zai sauke, saboda duk irin yadda ka ci burin yin nasara, zaka iya samun sabaninta bana.Tun daga za6en fidda gwani sun gane matsayinsu a siyasance. Wasu da yawa anyi za6en fidda gwani an tinkasu da kasa da magudi ko da kuri’a.
Misali,akwai sanatoci da gwamna sukutun-da-guda da suka sha kayi a Najeriya.Lallai kallo ya koma sama,wasan ya koma hannun dattijai.
An guji dattijo an hadu da fishin wani dattijon.
Allah cikin ikonsa,ana zaton wuta a makera sai aka sameta a masaka. Jam’iya mai mulki tayi za6en fidda gwani ta gama duk da cewa an samu korafe-korafe da koke-koke a kusan ko ina a kasar.
Wasu suna ganin gwamnoni sun ci karensu babu babbaka,wannan ne ya fusata ‘yan siyasa da yawa,wasu suke kokarin komawa qananan jam’iyyu,wasu kuma suna cikin tasu jam’iyar a matsayin ‘yan uba don haka a shirye suke su yi anti-party.
Amma za a iya samun fitar kafa daga wajen irin wadannan fusatattun ‘yan siyasa idan har za a tafi da sakamakon da su suke gani a matsayin magudi. Wannan a iya jam’iya mai mulki kenan kafin mu dubi babbar jam’iyar adawa ta PDP.
A rana ta shida ga watan October na wannan shekarar,’ya’yan jam’iyar PDP suka tafi garin Fatakol don yin nasu zaben fidda gwani wanda kamar yadda ya tabbata tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya (Atiku Abubakar) ne yaci zabe.
A yayin da ya tserewa manyan matasan ‘yan siyasar Najeriya masu matsayi kusan ‘daya ta fuskar girma a siyasa. Wannan sakamako ya bawa magoya bayan tsohon gwaunan Kano da kuma na Jigawa da kakakin majalisa mai ci da kuma gwaunan Sokoto da Gombe (Kwankwaso,Tambuwal,Lamido,Dankwambo da Saraki) mamaki duba da yadda suka nuna buqatarsu a fili ta son shugabancin Najeriya
Tabbas kallo ya koma sama,abun tambaya a nan shine,shin akwai amfanin badi idan baka da rai? Na farko dai sun guji Buhari sun koma jam’iyar adawa kuma gashi sun sha kasa. Da mamaki yadda matasan ‘yan siyasa kamar su Kwankwaso suka sha naushi a hannun dattijo ‘dan shekara saba’in da biyu.
Mutane da yawa idan aka ce Atiku zai ci zabe ba zasu yadda ba saidai kawai zasu ce maka yana da kudi da kuma yara a Najeriya amma wasu suna ganin kamar bashi da ‘structure’ irin ta su Kwankwaso.
To menene ya kawo masa nasara? Kudi? Structure? Ko kuma suma PDP din anyi magudi? Gaskiya dai kallo ya koma sama.Tabbas a zabe mai zuwa dattijai ne zasu gwada qwanji, Buhari da Atiku tunda dama ta safe ance ta yaro ce.Talakawa ku shirya tsaf da addu’a da kuma shirin gina sabuwar Najeriya.
Allah yasa mu ga Alheri.