SHANYEWAR BANGAREN JIKI: Alamu 7 da za a maida hankali a kai

0

Ranar 29 ga watan Oktoba rana ce da ake kira ranar ciwon shanyewar bangaren jiki wanda a dalilin haka kungiyar WSO ta yi amfani da wannan rana domin wayar wa mutane kai game da cutar da hanyoyin da za a kiyaye.

WSO ta ce mutane ‘yan kasa da shekara 65 ne ke kamuwa da cutar sannan mata sun fi maza kamuwa da ita.

Likitoci sun bayyana cewa bangaren jikin mutum kan shanye ne idan jini ya kasa wucewa ta wani jijiya saboda sandarewa sannan yawan kitse a jiki, shan taba, giya,yawan damuwa, kamuwa da cututtukan dake kama zuciya na cikin abubuwan dake kawo wannan cutar.

Bincike ya nuna cewa kasashen da ke tasowa ne suka fi fama da cutar kuma mutane kan rasa rayukan su ne a dalilin kamuwa da cutar saboda matsalolin rashin sani da talauci.

Alamomin wannan cutar sun hada da:

1. Makanta a duk idanuwa ko kuma ido daya.

2. Rashin iya motsa bangaren jiki

3. Yawan jin gajiya a jiki

4. Yawan rudewa

5. Mutum ya kasa iya yin Magana

6. Rashin gane maganar mutane

7. Jiri

WSO ta yi kira ga mutane cewa da zarar sun ji irin wannan alamu su hanzarta zuwa asibiti.

Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnatocin kasashen duniya da su ci gaba da yiwa mutane gargadi da wayar musus da aki game da cutar sannan a taimaka musu da asibitoci da magungunan da suke bukata wajen kula da masu dauke da wadannan.

Share.

game da Author