Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta yi kira ga kasashen nahiyar Afrika kan su kara zage damtse wajen ganin sun kawar da cutar shan-inna daga kasashen su.
Shugaban WHO Matshidiso Moeti ya bayyana haka a taron ranar cutar shan-inna da ake yi duk ranar 24 ga watan Oktoba sannan ya kara da cewa hakan zai samar wa kasashen damar hana bullowar cutar.
Idan ba a manta ba a shekarun baya Najeriya ta yi fama da yawan bullowar cutar shan-inna musamman a yankin arewa maso gabashin kasar.
Bincike ya nuna cewa cutarta ki karewa a wannan yanki ne a dalilin aiyukkan Boko Haram inda hakan ke hana ma’aikatan kiwon lafiya yi wa yara allurar rigakafin cutar.
Jami’in WHO Adamu Ningi yace bincike ya nuna cewa rashin kammala yin allura da rashin yin allurar kwata-kwata na cikin matsalolin daya sake bullo da cutar.
Moeti yace a dalilin haka yake kira ga kasashen Afrika da su mai da hankulan su wajen ganin sun kawar da wannan cutar.
” Rashin mai da hankali wajen kawar da wannan cuta a Najeriya na jefa sauran kasashen yankin Afrika cikin matsalar kamuwa da cutar.
Discussion about this post