SHAKAR GURBATACCIYAR ISKA: Mutane miliyan bakwai ke mutuwa duk shekara a duniya – Binciken WHO

0

Bincike ya nuna cewa mutane miliyan bakwai ke rasa rayukan su a duniya a duk shekara a dalilin shakar gurbataciyar iska.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta gano haka inda ta bayyana cewa ya zama dole duniya ta dauki mataki domin dakile illolin dake tattare da shakar gurbayaciyar iska.

Binciken ya kuma kara nuna cewa shakar irn wannan iska na kawo cututtuka kamar su dajin dake kama huhu, shanyewar bangaren jiki, cututtukan dake kama zuciya da sauran su sannan adadin mutanen dake mutuwa a dalilin kamuwa da cutar sun kai a kalla kashi daya bisa uku a duniya.

WHO ta bayyana cewa aiyukkan noma, masana’antu, makamashi, hayakin ababen hawa, hayakin risho, tara bola na cikin abubuwan dake gurbata iska sannan hakan na kawo canjin yanayin dake cutar da kiwon lafiyar mutum.

Kungiyar ta ce domin shawo kan wannan matsalar ne za ta shirya taro domin daukan matakan da ya kamata su dakile wannan matsalar.

” Za a fara wannan taro ne a ranar 30 ga watan Oktoba zuwa ranar daya ga watan Nuwamba a Geneva, Switzerland.

” Kungiyoyin kare muhali, ma’aikatar kiwon lafiya, ma’aikatar sufuri, makamashi da sauran su za su halarci wannan taron.

A karshe WHO ta ce taron zai tattauna hanyoyin da suka fi dacewa domin kawar da wannan matsalar a duniya gaba daya.

Share.

game da Author