Sansanin gudun hijira ya zama sansanin lalata da mata –Malamar Jami’a

0

Wata mai bincike ta musamman da ke aiki a wata cibiya, mai suna Rasheeda Liman, ta bayyana Sansanonin Masu Gudun Hijira a Jihar Barno cewa sun zama sansanonin da ake cin zafafin mata ta hanyar yin lalata da su ko yi musu fyade, musamman ‘yan matan da ba su kai ga yin aure ba, wadanda sun dogara ne da sai an ba su abinci domin su rayu.

Ta ce mafi yawan lokuta kafin a bai wa mata abinci sai an yi lalata da su ko kuma an ci zarafin su ta hanyar tirsasa yi musu fyade tukunna.

Rasheeda ta yi wannan jawabi ne a wani taron makomar mata, a Ranar Kananan Yara Mata ta Duniya, da aka gudanar a Zaria, wanda Kungiyar WCI ta shirya.

“Ya kamata gwamnati ta kawo karshen cin zarafi da fyaden da ake yi wa mata. Ana tilasta wa yara mata har wadanda ba su wuce shekaru tara ba yin karuwanci a cikin sansanin ‘yan gudun hijira.”

Haka malamar jami’ar ta bayyana, wadda ke koyarwa a Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria.

Ta kara da cewa al’umma ta ki tausaya wa wadannan mata da ‘yan mata daga halin kuncin da suke ciki, maimakon haka, sai a rika bi ana lalata da su ko yi musu fyade kafin a ba su abinci.

Ta yi korafin cewa rashin wadataccen tsaro ke sa masu yi musu fyade da fashi da kuma yin lalata da wasu jami’an tsaro da ma’aikatan wurin ke yi da su.

Wadda ta shirya taron, Murjanatu Sulaiman Shika, ta ce maganar gaskiya ba a bai wa mata da kananan yara mata kulawa da tsaron da ya dace ko ya wajaba a rika ba su.

Ta kuma nuna damuwar ta kan yadda yara maza a Arewa suka fi mata samun wasu damammaki na rayuwa da kuma zamantakewa a cikin al’umma, musamman batun ilmintarwa da sauran nau’o’in kulawa.

Share.

game da Author