Sanatocin APC sun yi watsi da batun tsige Saraki

0

Mambobin Majalisar Dattawa ’yan jam’iyyar APC sun yi watsi da kulle-kullen da suka rika faman yi da nufin tsige Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki.

Saraki ya hadu da fushin su ne tun bayan da ya fice daga APC ya koma PDP tare da wasu sanatoci da ‘yan Majalisar Tarayya da dama, ciki har da Kakakin Majalisar, Yakubu Dogara.

Wannan ya haifar masa da tsangwama daga sanatoci da dama da kuma shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, wanda ya rika kartar kasa cewa idan Saraki bai sauka ba, to ko da karfin tuwo sai an tsige shi.

Alamomin yin watsi da batun tsige Saraki sun fara ne tun a ranar Talata da majalisa ta koma daga hutu, inda ta shiga ganawa ta sirri. Bayan fitowar su ne suka nuna cewa sun amince su yi watsi da duk wata rikita-rikitar da za ta kawo tsaiko a majalisa.

Jiya Juma’a ne kuma Shugaban Masu Rinjaye, Sanata Ahmed Lawan ya bayyana wa manema labarai jingine batun tsige Saraki, bayan fitowar su daga taron ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari, a Fadar Shugaban Kasa.

“Ya kamata mu manta da sabanin da ke tsakanin mu, mu tsaya mu yi wa Najeriya aiki.”Inji Sanata Lawan.

Lawan ya ce sun yi wannan shawara ce domin su tabbatar da cewa Shugaba Buhari bai rika samun tarnaki ko tsaikon amincewar wasu batutuwan da ya ke so majalisa ta amince ba.

Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ta taba yin nazari, inda ta nuna cewa matsawar a kan ka’idar da doka ta gindaya za a bi, to Sanatocin APC ba za su iya tsige Saraki ba.

Share.

game da Author