Kungiya mai zaman kan ta ‘AIDs Health Foundation (AHF)’ ta bayana cewa ta sami nasarar samar wa mutane sama da miliyan daya a duniya maganin kawar da cutar Kanjamau.
Kungiyar ta fadi haka ne ranar Alhamis a taron cika shekaru 31 da fara aiki inda ta bayyana cewa a yanzu tana da ofisoshi 41 a kasashe dabam-dabam a fadin duniya.
” Ina cike da murna yadda kungiyar mu ta iya samar wa wadanda ke dauke da cutar Kanjamau kula. Hakan yayiwune bayan maida hankali da muka yi da tabbatar da mun kara bude ofisoshi domin isar wa mutane da aiki.
Weinstein ya bayyana cewa yanzu babbar burin su shine yadda za su ci gaba da samar da maganin wa sauran mutane dake dauke da wannan cutar a duniya.
A karshe shugaban hukumar hana yaduwar cutar Kanjamau na kasa(NACA) Sani Aliyu ya jinjina wa kungiyar AHF bisa kokarin da take yi inda ya hore su da su ci gaba da wannan aikin da suke yi ganin cewa abin na taimakawa matuka.
Discussion about this post