A yau Litini ne ma’aikatan hukumar inshorar lafiya ta kasa NHIS suka yi cirko-cirko a wajen ofishin inda suka garkame kofar shiga don hana dakataccen shugaban hukumar, Yusuf Usman shiga harabar ma’aikatar ballantana ya kai ga ofishin sa.
Idan ba a manta ba a ranar Alhamis ne shugaban kwamitin gudanarwa na hukumar Enyantu Ifenne ta sanar da dakatar da Yusuf daga aiki sai Illa-masha’Allahu.
Kwamitin ta dauki wannan mataki ne bisa ga laifuka tara da Yusuf ya aikata a hukumar.
Enyanatu ta ce wannan matsaya da suka dauka zai samar wa kwamitin da suka kafa damar gudanar da bincike kan laifukan da Yusuf ya aikata.
‘‘Sannan mu ba Yusuf damar tattara inasa inasa daga ofishinsa ranar Juma’a domin kwamitin ta sami damar gudanar da aiyukkan ta yadda ya kamata.
Sai dai kuma tun da sanyin asuba, Yusuf karyata wannan zargi da ake yi masa sannan a yau Litini ya tunkari ofishin sa da ‘Yan sanda kusan 50 inda da karfin tsiya suka shigar da shi ofishin sa.
” Sun yi mana feshin barkonon tsohuwa sannan sun yi kokarin harbin mu domin mun hana shi shiga ofis’’. Inji shugaban kungiyar ma’aikata, Omameji Abdulrazak.
Bayanai sun nuna cewa har yanzu fadar shugaban kasa ba tace komai ba a kai sannan a kwai rade-radin cewa Yusuf na aikata abinda ya ga dama ne bisa ga sanayyar fadar shugaban kasa.
Discussion about this post