Rikicin Shi’ah da Sojoji a Zuba, mutane uku suka rasu

0

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa ‘yan Shi’ah uku ne suka rasu a gumurzu da aka yi tsakanin mabiyan shi’ah da sojojin Najeriya a garin Zuba.

Daruruwan mabiya ne suka tate hanyar Zuba zuwa Abuja ranar Asabar inda suka hana motoci wucewa.

A daidai suna haka ne sai kuma ga tawagar wasu motocin sojoji dauke da makamai za su kai Kaduna.

Kwamandan Barikin Soji dake Abuja, James Nyam, ya ce da sojojin suka iso wannan wuri sannan suka nemi ‘Yan Shi’an su basu hanya su wuce sai suka ki.

” A daidai wannan tawagar sojoji na kokarin ganin wadannan masu tattaki sun kauce da ga hanyar ne, sai suka fara harbe harbe da duwatsu da makamai.

” Suka rorrotsa wa mutane da sojoji motoci sannan suka nemi kai wa gare su. Daga nan ne fa sojojin suka nemi karin ma’aikata domin kare kan su da makaman fa suke tafe da.

Daga karshe aka fatattaki masu tattakin aka baza su sannan matafiya da su kan su sojojin suka kama gaban su.

Share.

game da Author