Tsakurowa daga jawabin Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, a Taron Sarakunan Jihar da aka gudanar a Gidan Sir Kashim Ibrahim, ranar Talata, 23 Ga Oktoba, 2018.
1 – Al’ummar gari, unguwa ko yanki da aka kone kadarori, gidaje ko dukiya ne za su biya kudin gyara abin da aka kone ko aka lalata.
2 – Gwamnati za ta yi amfani da Dokar Hana Tashe-tashen hankula ta 1958, ta 1915 da ta 1917 domin tabbatar da ana hukunta masu laifi kuma zaman lafiya ya samu.
3 – Gwamnatin Jihar Kaduna ba za ta sake karba ko lamuntar wani uziri daga sarakunan gargajiyar da rikici ya barke a yankunan su ba. Gwamnati ba za ta sake yarda wani basarake ya ce wani takadari ko gungun ‘yan iska sun fi karfin sa ba.
4 – Daga garin Kasuwan Magani tushe da asalin rikice-rikice da kashe-kashe ya samo asali a jihar Kaduna, cikin 1980. Tun daga lokacin wasu gani suke yi ko sun tayar da fitina babu abin da zai faru, hukunci ba zai biyo baya ba.
5 – Yanzu ne lokacin da za a yi taron-dangin tabbatar da wanzar da zaman lafiya a kan masu ganin su na da karfin hana al’umma rayuwa cikin kwanciyar hankali da lumana.
6 – Mutane 22 aka kashe a rikicin da ya barke cikin Kaduna a ranar Lahadi da ta gabata, wasu 44 suka ji rauni, an kuma lalata kayayyaki da kadarori masu tarin yawa.
7 – Za a tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da hannu a cikin tashe-tsashen hankulan. Kuma Gwamnatin Jihar Kaduna za ta nemi amincewar Hukumar Kula da Fannin Shari’a ta Kasa (NJC), ta amince Kaduna ta kara daukar alkalai 20 domin a samu saukin rika gaggauta yanke hukunci a kotuna.
8 – Gwamnatin Jihar Kaduna na aiki kafada-da-kafada da runduar ‘yan sandan jihar Kaduna, domin ganin an gina ofishin ‘yan sanda a Narayi da Sabon Tasha.
9 – Ana ci gaba da sake gina Kasuwar Kafanchan, kuma za a sake gina kasuwannin Zonkwa, Zangon-Kataf, Kasuwan Magani da ta Kujama. Za a maida su na zamani, duk mai shago a ciki zai samu abin sa, kuma wasu da ba su da shaguna a ciki za su samu. Kuma za a gina ofishin ‘yan sanda a kowace kasuwa.
10 – Abin takaici ne har yau ba a gyara wuraren ibada da aka kone ba tun lokacin rikicin 2011. Mu na son cimma batun sake wa wadanda rikicin ya shafa matsugunai, biyan diyyar rikicin 2011 da ba a karasa ba har yau.
11 – Don haka mu na tuntubar gwamnatin tarayya kan batun cikon sauran kudade har kashi 53 bisa 100 na sauran diyya da kuma batun gyara wuraren da aka lalata.
12 – Motocin gwamnati na KSTA tare da rakiyar jami’an ‘yan sanda da Civil Defence za su rika raka matafiya wajen Kaduna fita garin daga tashar jirgin kasa da kuma filin jirgin sama, tashoshin mota da kuma masu shigowa cikin gari.
13 – ‘Yan sanda su kara sa-ido wajen hana baburan acaba zirga-zirga domin har yanzu dokar haramcin su na nan daram.