RIKICIN KADUNA: An dakatar da safarar fasinjoji na jirgin kasa daga Kaduna-Abuja

0

Hukumar jiragen kasa ta kasa ta sanar da dakatar da safarar fasinjoji daga Kaduna zuwa Abuja har sai an samu dawowar zaman lafiya a Kaduna.

Shugaban hukumar Fidet Okhiria ne ya sanar da haka yana mai cewa hukumar ta hakura da ci gaba da jigilar fasinjojin ne saboda rashin zaman lafiya da ya ki ci yaki cinyewa a garin Kaduna.

Ya kara da cewa jiragen kasan ba za su yi aiki ba har sai an janye dokar hana walwala da aka saka a garin Kaduna sannan zaman lafiya ya dawo.

Har zuwa ranar Lahadi 28 ga wata dai, ana zaman kulle na a garin Kaduna da kewaye a dalilin doka da aka saka na hana zirga-zirga a fadin jihar.

Share.

game da Author