RIKICE-RIKICEN AREWA: Tsakanin Rabeh, Bukar Amadidi, Shekau, Rikicin Kabilanci, Makiyaya da Mahara

0

Tun farkon kafuwar dauloli a yankin da a yanzu ake kira Arewacin Najeriya, ake fama da kashe-kashen yake-yaken cin garuruwa da sarakuna da dauloli ke yi, domin fadada masarautun su ko kuma wasoson dukiyoyi da kamen bayi domin habbaka tattalin arzikin yankunan su. Ba kuma Arewa ce kadai ta yi fama da wannan bala’i ba – ruwan dare ne, ya gane ko’ina a duniya, sai dai a ce wasu daulolin ko yankunan sun riga wasu fita daga cikin wannan mummunan yanayi.

Jihadin Shehu Usmanu ya samu ana turnukun yake-yake a Arewa, tare da kamen-bayi, hare-hare da babu iyaka.

Daular Shehu Usmanu ba ta kafu ba sai da Arewa, musamman yankin Sakkwato da Zamfara da sauran daulolin Arewa ta yanzu suka tirnike da yake-yake.

Sai dai kuma Daular Usmaniyya wadda ta kwace mulki daga hannun Sarakunan Habe ta maye gurbin su kaf da Sarakunan Fulani, ta shimfida tsari na mulki da yadda ake tafiyar da gwamnati har zuwa tsarin zamantakewa da na shari’a. Duk da dai hakan bai haifar da bunkasar ci gaba sosai ba, saboda su kan su sarakunan a tsakanin su sun ci gaba da yakar junan su a gumurzu daban-daban da muka rika karantawa a litattafan tarihi da dama.

Su ma Turawan mulkin mallaka da karfin tsiya suka kutso kai cikin yankin da ake kira Arewa a yanzu, an sha fama da yake-yake a garuruwan sarakunan da duk suka tunkura kafin su Turawan su ci su da karfin makamai.

Tsarin mulkin Turawa ya shimfida gwamnatin mulkin mallaka, wadda ta fara samar da wasu abubuwan da kafin sannan sai a kasashen Turai kadai ake samun su. Daga nan ne aka fara ganin alamomin kamo turbar ci gaban al’umma, daga tsallen da aka shafe shekaru daruruwa ana yi wuri daya.

RIKICE-RIKICEN KASHE AREWA

Cikin shekarar 1893, wani hatsabibin sojan kasar Sudan ya balle tare da zaratan sojoji mabiyan sa har su 2,000, ya shigo kasar Barno da mayaka masu bindiga 1,500, da wasu 500 kan doki da manyan bindigogin igwa ta wancan zamani har guda biyu. Rabeh da sojojin sa su na tafe su na ruguza duk wani gari da suka tarar kan hanyar su kuma su na sace matan garin kafin su yi gaba.

Da Shehun Borno Hashim ya samu labarin shigowar Rabeh kasar sa, ya tura mayaka 3,000 amma suka kasa arangama da su, suka gudu. Ya sake tura soja 6,000 suka hadu da na Rabeh a Ngala, nan ma suka gaza suka gudu Kukawa, inda Rabeh da sojojin sa su ka bi su a Kukawa, ya kama garin. Wannan kusan ya zame sanadin juyin mulki da Kyari ya kashe Hashim ya zama sabon Shehu. Da Kyari ya kai wa Rabeh farmaki, sojojin sa sun yaudari na sabon Shehun suka gudu, amma suka dawo cikin dare suka kai harin bazata, karshen ta suka kame Shehu Kyari. Rabeh ya tare a garin Dikwa tare da matayen da ya kama.

Rabeh ya yi shekara bakwai yana mulkin kama-karya a kasar Barno da kewaye daga mazaunin sa a Dikwa. Sai da Turawan Faransa suka shigo karkashin shugabancin Amedee-Francois Lamy (wanda aka rada wa garin Ndjamena, babban birnin Chadi sunan sa da farko, wato Fort Lamy), a shekara ta 1899.

Da Rabeh da Lamy sun yi ta sa-in-sa, karshe suka yi gumurzu a yakin Kousseri a cikin kasar Kamaru inda dukkan su biyu suka rasa rayukan su, amma Faransawa suka yi nasara. Kusan ana iya cewa yakin Kuousseri ya kawo karshen wasoson mallakar kasashe da kasashen Turai ke yi a Afirka a wancan lokacin.

Ana cewa wani tsohon sojan Rabeh mai suna Samba Sall ne ya kashe shi. Shi Samba Sall ya bar Rabeh ya shiga rundunar sojan Faransa bayan maigidan na sa na da ya azabtar da shi, har da dauri dalilin wani karamin laifi. Da aka ce wa Faransawa Rabeh ya mutu, da farko kin yarda suka yi, saboda an sha ikirarin cewa ya mutu daga baya a tarar ba haka ba ne. Ko da aka kawo wa Janar din Faransa mai suna Gentil kan Rabeh, kin yarda ya yi shi ne sai da Samba Sall ya tabbatar masa da hakan.

Rikici da wadannan sojojin Rabeh bakin haure bai kare a nan ba, domin kuwa ya sami magaji, dansa Fadlallah. Sai da sojojin Faransa suka tsallaka bangaren kasar Kamaru da ke karkashin Jamus, suka shigo Nijeriya mallakar Turawan Ingila, sannan suka fafari Fadlallah suka kashe shi.

FITINAR BUKAR AMADIDI A DAULAR BARNO

A cikin 1937, wani shahararen dan fashi da makamai mai suna Bukar Amadidi, ya addabi mutanen yankin da ya kama daga Damboa zuwa Chibok da Gwoza, har zuwa cikin kasar Kamaru. Idan shi da magoya bayan sa suka tare matafiya suka yi musu fashi, ya kan baIwa wasu ‘yan uwan sa ‘yan kabilar Gamergu domin ya dadada wa al’umma su rufa masa asiri.

A wancan zamani Turawan Birtaniya na mulkin Nijeriya na Faransa na mulkin Kamaru. Bukar Amadidi kan shiga kauye a bangaren Nijeriya ya sa wa kowane magidanci haraji, ya kuma ketara Kamaru inda ba mallakar Birtaniya ba ne, ko kuma ya yi ta’adi a Kamaru ya ketaro yankin Barno, mallakar Birtaniya. Ya yi ta kashe mutane da dama, aka rasa yadda za a yi da shi.

Da jami’an gwamnatin Birtaniya da na Faransa suka fahimci cewa Bukar Amadidi zai ci gaba da yin wasan kulli-kurciya da su, kasancewar iyakar kasashe, sai suka shirya zama a garin Marwa da ke Kamaru, inda suka yi yarjejeniyar da ta ba wa junan su izini su fafare shi da magoya bayan sa har cikin kasashen juna. A dalilin haka Faransawa suka shirya da Sarkin Mora ya nemo maharba ‘yan farauta, suka gano inda Bukar Amadidi yake suka yi masa kwanton bauna suka bindige shi da wasu mukarraban sa guda biyu har lahira.

Karshe aka daure gawarwakin su a kan bajimin sa, aka damka wa D.O ma’aikacin gwamnatin Birtaniya na mulkin mallaka da ke zaune a Mora. A wancan zamanin, Turawa ba su riga sun karfafa kiyayewa da ‘yancin bil Adama ba, saboda haka suka yanke kawunan Bukar Amadidi da ‘yan koran na sa biyu suka tsire su a kan sanduna gaban ofishin D.O domin ya zame gargadi ga al’umma baki daya.

Jami’an gwamnatin Faransa sun rubuta wa gwamnatin Birtaniya wasikar godiya da taya murna da suka ba su izinin biyo Bukar Amadidi cikin kasar su aka yi maganin wanda ya shige wa su biyun hanci ya matsa wa al’umma lamba.

Cikikakken wannan bayani duk ya na cikin wata makala da Yusuf Tuggar ya taba rubutawa a cikin wani filin sa mai suna “Barandami”, cikin 2014, inda ni ma a can na tsakuro.

YADDA FITINA DAGA GABAS KE KASSARA AREWA

Idan mai kararu na biye da ni tiryan-tiryan, zai fahimci yadda fitintinun da suka kassara Arewa suka fara kunno kai daga gabacin Najeriya. Ga dai Rabeh da ya mamaye Daular Barno daga Sudan, dan sa Fhadallah, ga Bukar Amadidi daga yankin Damboa da Gwoza a Barno.

Daga nan sai kuma fitinar Maitatsine, ita ma da ta kunno kai a Arewa, daga wani hatsabibin malami, mai suna Muhammadu Marwa, da aka fi sani da suna Maitatsine, wanda ya fito daga garin Marwa, cikin kasar Kamaru, ya yi kaka-gida a Kano, a farkon mulkin tsohon Shugaban Kasa, Shehu Shagari, cikin 1980.

An ci karfin Maitatsine, bayan ya yi wa tattalin arzikin Kano da Arewa mummunar illa. Sai dai kuma ya tafi ya bar baya da kura, domin ya cusa wa matasan Arewa da suka rika yin karatun allo a karkashin sa mummunar akidar addini, wadda har yau ba ta daina tasiri a zukatan matasa da dama ba.

FITINAR BOKO HARAM DAGA BARNO

Sabuwar fitina ta sake kunno kai daga Barno, sama da shekaru ashirin bayan ta Maitatsine. Boko Haram, wadda tun bayan mulkin mallaka ba a taba samun mummunar fitina a Afrika ta Yamma kamar Boko Haram ba, a yau ta na a sahun gaba wajen kassara tattalin arzikin Arewa.

Da ya ke fitina ce wadda a kullum mu na cikin ta a Arewacin kasar nan, ba ta da bukatar dogon sharhi, domin kusan babu wanda bai ji ta a jikin sa ba. Babban abin takaici a nan, alamomi na nuna tabbas babu rana ko shekarar da za a iya kakkabe wannan fitina.

Sai dai kuma wani abin lura, wadannan fitintinu da na lissafa wadanda suka kunno mana daga gabas, duk kusan sun yi kama da juna, domin babu wadda sata, fashi, kwace, samame, hare-haren kama jama’a, banka wa gidaje wuta da yin garkuwa da mutane bai yi tasiri a cikin su ba.

Dubban mutane sun rasa rayukan su, an sace daruruwa, an tilasta da dama zaman sojan Boko Haram, an kassara Arewa sosai ta hanyar jefa bama-bamai babu iyaka, an rasa dukiyoyi na bilyoyin nairori. An yi asarar daruruwan sojoji, gwamnati a kullum ta na kashe bilyoyin nairori wajen kokarin dakile Boko Haram. An lalata daruruwan garuruwa da kauyuka. Duk a Arewa.

RIKICE-RIKICEN KABILANCI

Wannan ma ba shi bukatar yin wani dogon sharhi, domin a cikin shekaru 38 zuwa yau, an kashe dubban jama’a tsakanin yankin Filato, kudancin Kaduna, Kano, Benuwai, Taraba, garin Kaduna da sauran garuruwan Arewa da na yankin ‘Middle Belt’ da dama.

Har yau kuwa wannan rikici sai kara ruruwa ya ke yi ta hanyar ta hanyar kara wa gashin sa tsawo, ya na yin rassa zuwa rikicin addini da na kabilanci.

RIKICI DA MAKIYAYA

Cikin shekaru bakwai zuwa yau, Allah kadai ya san iyaka ko adadin dubun-dubatar shanun da Fulani makiyaya suka yi asara daga hare-haren barayin shanu da kuma fadace-fadacen kabilaci. Satar shanu ta yi tasiri sosai wajen karya tattalin arzikin Fulani makiyaya a jihar Katsina, Zamfara, Kaduna da sauran jihohin Arewa kama daga Taraba, Adamawa, Barno da dukkan jihohin yankin ‘Middle Belt.’

Asarar rayukan da aka tafka sanadiyyar fadace-fadacen manoma da makiyaya ta yi muni kwarai a kasar nan, kuma ta shafi tattalin arzikin Arewa. Sannan kuma babu alamar rana ko lolacin da za a iya shawo kan wannan rikici.

MAMAYAR MAHARA A AREWA

Duk da kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na yin amfani da sojoji wajen dakile fitintinun cikin gida, hakan bai kawo karshen hare-haren da ake fama da su a fadin Arewacin kasar nan ba. A Najeriya dai akwai girkakkun sojojin da gwamnati ta kafa a jihohi har 32, daga cikin jihohi 36 da muke da su a kasar nan, da kuma FCT, Abuja. Amma hakan bai haka mahara, ‘yan ta’adda da samame cinnkaren su babu babbaka ba.

A yau a Arewa fashi da makami na neman zama tarihi, domin barayi sun fahimci mummunar sana’a ce mai hatsari a gare su. Muggan masu laifi gaba daya sun karkata mummunar sana’ar su wajen hare-hare da garkuwa da jama’a.

Tun da farko Fulani ne aka fara kassarawa ta hanyar hare-haren sace musu shanu ana banka wa rugagen su wuta, bayan an karkashe su. Har fitinar yanzu ta kai ana dira gari ko kauye a karkashe jama’a, a kwashi dukiya, a banka wa kauye wuta, ko kuma kawai tare hanya a rika yin garkuwa da jama’a.

Kamar yadda babu ranar da rana ba za ta fito daga gabas ba, haka kuma babu ranar da ba za a yi garkuwa da jama’a a Arewacin kasar nan ba. Idan ba a tare mutum a hanyar Abuja ba, to za a tare shi a hanyar Birnin Gwari, ko Zamfara, ko yankin kudancin Kaduna da sauran hanyoyi da dama. Abin ma ya kai har gida-gida ake sallama a tasa iyali ko maigida a gaba, a yi garkuwa da su.

Allah kadai ya san milyoyin kudin da jama’a ke asara a kullum wajen biyan diyyar ’yan uwan su da ake sacewa a na yin garkuwa da su a kullum. Allah kadai ya san wadanda ke halaka a hannun masu garkuwa da jama’a a kullum. Allah kadai ya san makudan kudaden da masu garkuwa da jama’a ke Tarawa a kullum. Allah kadai ya san tattalin arzikin da ake gurguntawa a Arewa a kullum. Kuma Allah kadai ya san ranar da za a iya kawo karshen wannan mumunar fitina. Sannan kuma Allah ya kare mu!

Share.

game da Author