Oshiomhole dan gada-gada ne -Shugaban VON

0

Babban Daraktan Gidan Radiyon Muryar Najeriya (VON), mallakar Gwamnatin Tarayya, Osita Okechukwu, ya zargi Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshimhole da cewa ya wuce-gona-da-iri sosai wajen haddasa rigingimun da suka dagula jam’iyyar a lokacin zabukan fidda-gwanin ‘yan takarar jam’iyyar ta APC.

Osita ya fito takarar sanata mai wakiltar Enugu ta Yamma, a karkashin APC, amma bai yi nasara a zaben fidda gwani ba.

A cikin wata rubutacciyar takarda da ya sa wa hannu da kan sa, kuma ya aiko wa PREMIUM TIMES, Osita ya nuna cewa babu komai a kwakwalwar Oshimhole sai burga, ji-ji-da-kai da kuma fankamar nuna cewa shi ma fa ya san komai.

Daga nan sai ya nemi Oshimhole da ya sauka daga shugabancin jam’iyyar, ya koma gida ya nemi gafarar zunubin da ya dauka na alhakin tsohon shugaban APC, John Odigie Oyegun ya Oshiomhole ya dauka.

“Shi fa gani ya ke yi kawai duk abin da ya yi, to kusan kashi 95 na jam’iyyar APC amince da hakan. Wannan wani kukumin tunani ne kawai irin nasa, ba gaskiya ba ne.

“Sannan kuma ya na nuna wa jam’iyya cewa Oyegun kayan sharri ne, shi kuma shi ne tulin alheri ga jam’iyya.

“Oshimhole ya sauka ya koma gida, can ya je ya nemi Oyegun gafarar laifin da ya yi masa, tun kafin ya ruguza mana jam’iyyar gaba daya. Ko yanzu din ma ya rigaya ya yi mata lahani.”

“In ba dan gada-gada ba ne shi, don me zai tsaida zaben fidda-gwani na Enugu ta Yamma, ana tsakiyar zabe, har an kammala zabuka a kananan hukumomi 4 daga cikin 17? Me ya hana shi bayar da wani sahihinn dalilin dakatar da zaben.”

Sannan kuma ya yi tir da Oshiomhole saboda yadda ya shige gaba aka nada sirikin gwamna Rochas Okorocha dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC na Jihar Imo.

Osita ya ce ai duk mutum mai hankali da lura da tunani, zai ji bambarakwai a ce Rochas Okorocha ya kammala zangon sa na biyu kuma an dora sirikin sa ya sake zama gwamna bayan shi.

“Sai Oshimhole ya fito ya shaida mana yadda za a yi APC ta sake kafa gwamnatin a jihar Imo, tunda ya rigaya ya karye mata fukafikin da za ta iya yin faffaka har ta yi gwauron tashi.”

Share.

game da Author