Hukumar Kula da Harkokin Mai ta Kasa (NNPC), ta bayyana cewa Najeriya ba ta da wani shiri na sarari ko na boye da ta ke yi, domin ganin ta karar farashin man fetur a fadin kasar nan.
Haka NNPC ta bayyana a cikin wata takardar manema labarai da kakakin hukumar, Nda Ughamadu ya raba wa manema labarai jiya Talata, a Abuja cewa zancen yiwuwar karin kudin man fetur ba gaskiya ba ne.
Ya ci gaba da cewa duk da cewa tun daga cikin watan Disamba na 2017 Najeriya shigo da mai ta ke yi daga kasashen ketare, wannan bai sa ta yi tunanin kara farashin litar man fetur ba, ko kuma sauko da shi kasa.
Ya ja hankalin ‘yan Najeriya da su guji yada jita-jita da kirkirar labarai na karairayi.
Ya shawarci masu yada irin wannan jita-jitar su daina, domin hakan na iya haifar da karancin fetur a lokacin bukukuwan hutun karshen shekara da Kirsimeti.
Daga nan sai ya kara jaddada albishir din shugaban NNPC, Maikanti Baru, inda ya ce a yanzu akwai fetur ajiye, wanda zai iya kai kwanaki 37 cur bai kare ba.