Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa yanzu ya yafe wa tsohon mataimakin sa Atiku Abubakar duk laifukan da ya yi masa a baya sannan ya yi masa fatan alkhairi da yi masa alkawarin mara masa baya a zabe mai zuwa.
Hakan ya biyo bayan ganawar sirri ne da tsoffin shugabannin suka yi a yau.
“ Lallai a shirin baya, Atiku ne zai gaje ni bayan na kammala zango na na biyu. Amma kuma a lokacin sai komai ya canja. Yanzu dai Atiku ya gane kura-kuran sa sannan ya gane cewa lallai ya tafka kuskure a baya. Amma yanzu tunda ya canja kuma ya roki tuba, na hakura kuma zan mara masa baya. Dama can abubuwan da yayi laifuka ne da ya shafi jam’iyya, Kasa da gwamnati mai ci a wancan lokaci.
“ A wancan lokacin da na yanke hukuncin sa kafar wando daya da kai, ban taba yin dana sani ba domin nayi haka ne saboda abinda ya dace da inyi Kenan.
“ Daga irin tattaunawar da muka yi da kai yau, ka yi nadama bisa ga laifukan da ka yi sannan ka yi da na sani akai kuma ya roki gafara nan take.
“ A matsayina na Kirista na gari da kullum yake rokon gafara a wajen Allah, na hakura kuma ina kwaban ka da ka dauki darasi daga abin da ya faru a aby aka gyara. Ka yi tafiya da duk ‘ya’yan jam’iyyar ka musamman wadanda su ka yi takara da kai.
“ Yanzu dai ka nuna cewa tabbas ka yi nadama. Kuma tabbas idan ka ci gaba da haka zaka yi nasara a abin da kasa a gaba. Kuma sauran wadanda ke suna da damuwa da kai, duka za su hakura yanzu. A haka ina maka tabbacin cewa idan kana da wani abu da kake so in taimaka maka da shi, ka gaggauta zuwa wuri na kokofina a bune suka da in taimaka maka.
“ Kafi duk sauran ‘yan takarar da kuka fafata a zaben fidda gwani kwarewa a siyasance da wayewa a farfajiyar siyasar Najeriya. Ka fi su zama zaki da karbuwa a fadin kasar nan. Na tabbata cewa ka fi zama wanda yafi dacewa ya mulki Najeriya fiye da wanda yake kan mulkin a yanzu. Ka fi wanda yake kai sanin tattalin arzikin kasa da bunkasa harkar kasuwanci da haka zai sa gwamnatin ka ya samu karbuwa matuka musamman a harkar kasuwanci da bunkasa tattalin arzikin kasa.
“ Ka samu karbuwa a kasar nan sannan zaka fi iya gyara hulda da zumuntar kasar nan da kasashen waje. Baka da tauri a al’amuranka sannan kai mutum ne da kowa naka ne.
Idan ka zama shugaban kasa ka koma baya ka gyara kura-kuran da aka yi. A haka za a tuna da mu cewa mun yi wa kasa hidima sannan mun saita ta kan hayar da ya dace.
“ Ina rokon ka da ka maida hankali wajen gyara kasa, ka rike gaskiya da amana, Yaki da cin hanci da rashawa, gyara dabi’un al’umma sannan ka maido da zaman lafiya a kasar nan.
“ Sannan ka tabbata ka yi biyayya ga dokar kasa sannan ka hada kan kasa. Ka sa jawo kowa a jika sannan ka jawo matasa kusa da kai a mulkin ka.