Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa Othman Abubakar ya bayyana cewa an rasa mutum daya sannan da dama sun sami rauni a rikicin da ta barke a karamar hukumar Lamurde.
Abubakar bai fadi sunayen kauyukan da wannan rikici ya faru ba amma ya ce bincike da suka yi ya sa sun gano cewa rikicin fa faro ne tun daga ranar Talata tsakanin wasu kauyuka dake yankin Lafiya.
Ya ce, an kona gidaje da dama.
” Rikicin ya barke ne tun bayan tsintar gawar wani a wata gona dake kusa da kauyen mamacin. Daga nan sa kawai mazauna wannan kauye suka far wa wannan kauye wai daukar fansa.
” Da ga jin haka ne kuma jami’an ‘yan sanda suka kai wa wannan kauye dauki maza-maza inda Allah ya sa aka shawo kan abin.
Jami’in ya ce sai dai basu kama kowa ba da zargin hannu a harin zuwa yanzu.
A karshe kwamishinan yada labarai na jihar Adamawa, Ahmad Sajoh ya ce gwamnati ta umurci hukumar bada agajin gaggawa na jihar (ADSEMA) da ta gaggauta kai wa wadanda suka fada halin kakanikayi a sanadiyyar wannan fitina tallafi.
Discussion about this post