An bayyana cewa kimanin mutane milyan 700 ne a fadin duniya ba su iya ciyar da kan su ballantana su iya daukar dawainiyar nauyin bukatun su na tilas, a kowace rana.
Shugaban Majalisar Dinkin Dinkin Duniya, Antonio Guterres ne ya bayyana haka a cikin wani rubutaccen sako da aika a Ranar Tunawa da Kokarin Kawar da Talauci a Duniya ta 2018.
Ya tunatar da cewa kakkabe fatara, yunwa da talauci na daya daga abin da ke kawo bazaranar kalubale a duniya.
Daga nan sai ya kara jaddada yin kiran cewa a hada hannu da aljihu a tabbatar da cewa nan da zuwa shekarar 2030 an cimma wannan muhimmin kudiri na kakkabe fatara da kuncin talauci a duniya.
Ya ce tun daga shekaru 25 da suka gabata da aka fara wannan shiri, kusan mutane bilyan daya sun fita daga kuncin talauci ta dalilin kafa gwamnatocin dimokradiyya, janyo al’umma a cikin gwamnati da kuma samun ingantacciyar gwamnati a kasashe da dama.
A yau Laraba ne Majalisar Dinkin Duniya a Hedikwatar ta da ke New York, Amurka, za ta yi bikin cika shekara 20 da fara yaki da fatattakar fatara, yunwa da talauci a duniya.