Masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya sunyi kira ga gwamnatin tarayya kan kara maida himma don kawar da zazzabin cizon sauron da kan sa kai yayi ta radadin gaske.
Gwanayen sun bayyana cewa zazzabin da kan sa kan mai dauke da ita yayi ta radadin gaske ya zama ruwan dare a Najeriya inda zuwa yanzu akalla mutane 100,000 ne aka gano suke kamuwa da cutar duk shekara.
Idan sauro ya ciji mutum sai ya zuba masa gubar wannan cuta a jikin sa da nan-da-nan sai kaga radadin ciwon kai ya dabaibaye mutum.
Alamomin wannan cutar sun hada da zazzabi, ciwon kai, zufa, rudewa da dai sauran su.
A karshe shugaban kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya (WHO) Tedros Ghebreyesus a madadin sauran masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya ya bayyana cewa dole ne fa sai an dai na nuna halin ko-in-kula game da wannan cutar kafin a iya shawo kan sa.