Muna kira ga gwamnati ta sa baki a kara wa asibitin mu fili – FMC, Legas

0

Shugaban asibitin ‘Federal Medical Center’ dake Ebute Meta jihar Legas Adedamola Dada ya roki ministan kiwon lafiya Isaac Adewole kan nema wa asibitin Karin fili daga wajen hukumar tashar jiragen kasa dake kasar nan.

Dada ya bayyana cewa asibitin na bukata wannan fili ne domin kara fadada girman asibtin don samar wa mutanen jihar kiwon lafiya yadda ya kamata.

” Mun fara da gyarar dakunan kwanciya,gadajen asibiti, bandakuna sannan muna kokarin ganin mun horas da ma’aikata da dai sauran su a dalilin karin marasa lafiya da ake samu.

Bayan haka da ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya ziyarci aisbitin ya jinjina aiyukkan da asibitin ke yi yana mai cewa ingancin kiwon lafiyar da za a samu bayan an kammala wannan gyare-gyare zai kai irin na asibitocin kasashen waje.

A karshe Adewole ya ziyarci asibitin da wasu shugabanin asibitocin FMC domin samu shawaran yadda gwamnati za ta iya kawo kaeshen matsalolin da ake fama da su a fannin kiwon lafiya.

Share.

game da Author