Ministan Abuja ya kai ziyara Mpape, yankin da dutse ya yi aman wuta

0

Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Mohammed Bello, ya kai ziyara garin Mpape da ke kusa da Abuja, inda wuta ta rika zubullowa da ga cikin wani tsauni a karshen makon da ya gabata.

Sai dai kuma Bello ya bai wa al’umma mazuna yankin tabbacin cewa su kwantar da hankalin su, babu wani abin da zai faru.

Ya ce ana ci gaba da binciken gano takamaimen musabbabin wutar.

A cikin wata sanarwa da kakakin yada labarai na ministan, Abubakar Sani ya sa wa hannu, ministan ya kai ziyarar tare da Karamin Ministan Ma’adinai da Karafa, Abubakar Bwari a ranar Talata.

Wutar da ta tashi a Mpape, ta fito ne makonni kadan bayan wata jijjigar kasa da aka yi a yankin, wadda har Abuja gaba dayan ta ta ji a jikin ta.

Masana sirrin muhalli da dama sun danganta jijijgar kasar da yawan fasa duwatsu da ginar rijiyoyin burtsatse barkatai da ake yi a yankin.

Daga nan ne aka haramta fasa duwatsu da ginin rijiyoyin burtsatse a gundumomin Maitama, Gwarimpa da Garki.

Kwatsam, karshen makon da ya gabata kuma sai mazauna Mpape suka tashi da wani sabon tashin hankali, inda aka ga dagwalon ruwan wuta na zababbakowa daga cikin wata kofar wani rami a wani tsauni.

An ce wutar a rika kankama har kan wasu tsaunukan.

“Mun ga hayaki na fitowa daga cikin daji, mun yi zaton ko wani naman daji ne, sai muka dauki dutse muka jefa wajen. Sai kawai ya kama da wuta.” Inji wani da ya ga wutar da idon sa.

Masana da dama sun jan kunne gwamnatin tarayya da ta daina yi wa batun jijjigar kasar da ta auku a Mpape rikon-sakainar-kashi.

Share.

game da Author