Kungiyar MPDRSR ta bayyana cewa a tsakanin watanni shida jihar Kaduna ta rasa mata 123 a wajen haihuwa.
Shugaban hukumar Lawal Abubakar ya sanar da haka ranar juma’a a zama da hukumar ta yi a Kaduna.
Abubakar ya ce sun gano haka ne a bayan sun gudanar da bincike a wasu asibitocin jihar guda 30.
” Asibitocin da muka ziyarta a wannan binciken sun hada da wadanda ke Kafanchan, Kachia, Kaura,Kagoma,Doka, Zangon Kataf, Kwoi da Kagoro.
‘‘Sauran asibitocin sun hada da na Pambegua, Zonkwa, Barau Dikko, Giwa, Yusuf Dan Tsoho, Birnin Gwari, Gwamna Awan,Kawo, Kawo, Rigasa, Kujama, Idon, Hunkuyi, Makarfi , MIBA Zaria, Zaria,Maigama da Turunku.
Ya ce bisa ga binciken an gano cewa manyan dalilan dake yin sanadiyyar rasuwar wadannan mutane sun hada da rashin isasshen jini a jiki, zubar da jini wasu cututtuka
Bayan haka Abubakar ya bayyana cewa asibitocin da suka ziyarta a jihar Kaduna na da magunguna wanda idan da an yi amfani da su wajen kula da wadannan mata da hakan bai faruwa.
Ya kuma ce sun gano cewa wadannan asibitocin na fama da rashin wutan lantarki wanda hakan ke hana su iya ajiye jini , rashin samun jini,rashin kayan aikin kula da matan da suka zubar da ciki a hannu likitocin da ba su da kwarewa da rashin motar daukan marasa lafiya.
Abubakar yace sun gabatar da sakamakon binciken su wa gwamnatin jihar Kaduna a ranar 18 ga watan Agusta domin daukan mataki.
A karshe kwamishinan kiwon lafiya na jihar Kaduna Paul Dogo yace gwamnatin jihar za ta dauki matakan rage yawan mace-macen mata a jihar musamman a sibitocin dake karkara.