Kungiyar malaman Najeriya (NUT) ta yi kira ga gwamnati da ta kara wa malamai yawan shekarun aiki daga shekaru 60 zuwa 65.
Shugaban kungiyar Muhammed Idris ya fadi haka a shirin bukin tunawa da ranar malamai ta duniya da ake yi duk 5 ga watan Oktoba.
Taken taron na bana shine ‘Samun ingantacciyar ilimi daga kwararrun malamai.”
Idris yace NUC ta zabe wannan take ne domin tsara hanyoyin rike kwararun malaman da kasar nan ke da su sannan da samo wasu kwararrun malamai domin inganta ilimin da al’uma ke samu.
Ya ce duk da haka malaman kasar nan na fama da wasu matsalolin da ya kamata a ce gwamnati ta magance su. Wadannan matsaloli kuwa sun hada da rashin biyan ma’aikata albashi mai tsoka domin karfafa guuwowin malamai kuma hakan zai sa mutane su yi sha’awar shiga aikin sannan da kara wa ma’aikata yawan shekarun aiki daga 60 zuwa 65.
Bayan haka jami’in ma’aikatar kiwon lafiya na gwamnatin tarayya Sonny Echono ya bayyan cewa gwamnati za ta ci gaba suba jari a harkar ilimi da inganta aikin malunta.
” Kamata ya yi a cewa adadin yawan shekarun aikin malamin jami’a, sakandare da firamare su zama daya amma ba na wani ya fi na wani yawa ba.”
Discussion about this post