Majalisar tarayya ta kafa kwamiti domin binciken rikicin hukumar NHIS

0

Majalisar dokoki ta kasa ta kafa kwamiti domin binciken rikita-rikitan da yaki ci yaki cinyewa tsakanin ma’aikatan hukumar Inshorar Lafita ta kasa da shugaban hukumar Usman Yusuf.

Diri Douye mai wakiltar jihar Bayelsa ya zagamar muhawarar a majalisar inda ya bayyana cewa abin yayi kamara da har sai da akai ta kai ruwa rana tsakanin ma’aikatan da shugaban hukumar, Yusuf Usman.

” Wannan shine karo na biyu da ake dakatar da Yusuf daga aiki kuma duk da haka yaki bin umarnin da kwamitocin dake dakatar dashi take bashi.

Douye yace a dalilin haka yake kira ga majalisar da ta gaggauta daukan mataki kafin hukumar ta zama filin yaki tsakanin shugaban ta da ma’aikatan hukumar.

Shima Tobi Okechukwu mai wakiltan jihar Enugu da yake tofa albarkacin bakin sa ya yi tir da abin dake faruwa a hukumar, haka shima Edward Pwajok dake wakiltan jihar Filato a majalisar ya yi kira ne ga majalisar da tayi ‘taka tsan-tsan wajen daukar matsaya game da abin da yake ta faruwa a ma’aikatar.

Share.

game da Author